Kamfanin Dangote ya faɗaɗa kai man fetur kyauta zuwa Kano da wasu jihohi domin saukar da farashin man a gidajen mai
Daga Wakiliya
Kamfanin Dangote Refinery ya faɗaɗa shirin kai man fetur kyauta zuwa Kano, Imo, Anambra da Nasarawa, domin rage kuɗin safarar man fetur da kuma samar da damar saukar da farashin man a gidajen mai.
Shirin ya fara ne da kai man fetur zuwa Lagos, Ogun, Rivers, Kaduna da Delta, da kuma Abuja.
Kamfanin ya ce ta hanyar ɗaukar nauyin kuɗin kai kayan, zai rage wani ɓangare na kuɗaɗen da ‘yan kasuwa ke kashewa wajen jigilar man fetur daga matatar zuwa wuraren sayar da shi.
Daraktar Gudanar da Kasuwanci ta Kamfanin Dangote, Fatima Aliko-Dangote, ta ce manufar shirin ita ce tabbatar da cewa fa’idar tace man fetur a cikin gida ta isa ga ‘yan kasuwa da masu amfani da shi.
Ta ce rage kuɗin rarraba man zai taimaka wajen rage wasu kuɗaɗen da ake ƙarawa kan farashin man fetur kafin ya isa ga masu amfani.
Ƙungiyar Independent Petroleum Marketers Association of Nigeria (IPMAN) ta yaba da matakin, inda ta ce zai rage matsin kuɗi da matsalolin sufuri da ‘yan kasuwar man fetur ke fuskanta.
Mai magana da yawun IPMAN na ƙasa, Chinedu Ukadike, ya ce shirin zai rage lokacin da kuɗin ‘yan kasuwa ke makale bayan sun biya kuɗin man fetur kafin a kai musu shi.
Ya ce idan aka ci gaba da shirin, zai iya taimakawa wajen rage farashin man fetur, musamman a wuraren da ke da nisa da matatar Dangote.
Chinedu Ukadike ya kuma yi kira ga Dangote Refinery da ta faɗaɗa shirin zuwa wasu sassan ƙasar, musamman jihohin Arewa.
Matatar Dangote tana da ƙarfin tace ganga 700,000 na ɗanyen mai a kowace rana, kuma tana ƙara samar da man fetur da sauran kayayyakin man fetur ga kasuwar Najeriya.
Ana sa ran rage kuɗin safarar man fetur zai ba ‘yan kasuwa ƙarin damar sauke farashin man a gidajen mai, idan aka samu ci gaba da rage kuɗaɗen da ke cikin tsarin rarraba man.




