1 cikin 4 na mazan da aka yiwa Gwajin DNA a Najeriya ba su ne ubannin yaransu ba – Rahoto

Gwajin DNA: 1 cikin 4 na mazan da aka yiwa Gwajin DNA a Najeriya ba su ne ubannin yaransu ba – Rahoto

Daga Wakiliya

Kusan mutum daya cikin maza hudu da aka yi wa gwajin DNA domin tabbatar da ubanci a Najeriya, an gano cewa ba su ne ubannin yaran da suke raina ba.

Wani rahoton kamfanin Smart DNA Nigeria ya ce kashi 23.6 cikin 100 na gwaje-gwajen DNA da aka yi a shekarar 2025/2026 sun nuna cewa mutanen da aka gwada ba su ne ubannin yaran ba.

Adadin ya ragu kadan daga kashi 24 cikin 100 a shekarar da ta gabata, da kuma kashi 26.1 cikin 100 a shekarar 2023.

Sai dai Smart DNA ta yi gargadin cewa wannan ba yana nufin cewa daya cikin maza hudu a Najeriya ba ubannin yaran da suke raina ba ne.

Kamfanin ya ce mutanen da suka je yin gwajin sun riga sun kasance da wasu dalilai ko shakku da suka sa suke son tabbatar da ubancin yaran.

Chukwudi Eze, Manajan Tallace-tallace na Smart DNA, ya ce ya kamata a kuma lura da cewa kashi uku cikin hudu na mazan da aka yi wa gwajin an tabbatar da cewa su ne ubannin yaran.

Mafi yawan gwaje-gwajen, wato kashi 87 cikin 100, mutane ne suka nema da kansu domin samun tabbaci kan dangantakar jini.

Rahoton ya ce maza masu shekaru 41 zuwa sama ne suka fi yawa cikin wadanda suka nemi gwajin, inda suka kai kashi 48 cikin 100.

Yara ‘yan kasa da shekaru biyar kuma sun kasance mafi yawan wadanda aka yi wa gwajin, inda suka kai kashi 59.5 cikin 100.

Lagos ce ta fi yawan gwaje-gwajen, inda ta kai kashi 75.1 cikin 100 na bayanan da aka tattara. Ogun ce ta biyo baya a jihohin da ke wajen Lagos.

Smart DNA ta ce ba za a iya amfani da sakamakon wajen tantance yawan yaran da ba ubanninsu na jini ba a Najeriya baki daya ba, saboda mutanen da aka yi wa gwajin ba su wakilci dukkan iyalan kasar ba.

Kamfanin ya kuma yi kira ga jama’a da su guji yada jita-jita ko amfani da wannan adadi wajen yin ikirarin cewa daya cikin maza hudu a Najeriya ba ubannin yaransu ba ne.

DA DUMI-DUMI

Farashin kayayyaki na raguwa a takarda, amma a zahiri farashin abinci na ƙaruwa, talakawa na fama da matsin rayuwa – Masana

Daga cikin matakan da ya ba da shawara akwai sakin hatsin da ke cikin rumbunan ajiyar gwamnati zuwa wuraren da ake fama da tsananin ƙarancin abinci, da kuma ɗaukar matakan gaggawa idan ambaliyar ruwa na cikin abubuwan da ke haddasa matsalar.

APC ta bukaci a binciki Dino Melaye da wasu jiga-jigan PDP kan zargin alaka da Dan Damfarar Intanet Hushpuppi

A wata sanarwa da Mataimakin Sakataren Yada Labarai na Kasa na APC, Yekini Nabena, ya fitar a Abuja ranar Asabar, jam’iyyar ta bukaci Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa (EFCC), da Hukumar Leken Asiri kan Harkokin Kudi ta Najeriya (NFIU), da sauran hukumomi su gudanar da cikakken bincike.

Bankaɗo tsoffin takardun zargin Tinubu na iya bata martabar Najeriya tare da yin tasiri a zaɓen 2027 – Buratai

Bankaɗo takardun tsofaffin laifukan da ake zargin Tinubu ko fitar da su na iya yin illa ga martabar Najeriya a idon duniya, sannan za su iya yin tasiri a zaben 2027 - Buratai ya bukaci 'yan Najeriya su yi watsi da zarge-zargen

Gwamnatin Birtaniya ta bukaci Musulmi su rage amfani da ruwa wajen alwala

Wasu masu fafutukar kare hakkin al'umma sun kuma ce Musulunci kansa ya yi kira da a guji barnatar da ruwa yayin alwala (almubazzaranci haramun ne a musulunci).

Kirista ya shiga Gasar Karatun Alƙur’ani a Masar, ya ci kyautar Umrah ya bai wa maƙwabciyarsa Musulma

Um Ali ta bayyana farin cikinta, inda Mina ya ce ya gan ta tana share hawayen farin ciki bayan ya sanar da ita cewa za ta samu damar zuwa Umrah.

Kanun Labarai

Gwamnatin Tarayya ta kulla yarjejeniyar farfado da Kamfanin Karafa na Delta cikin watanni 18 kan dala biliyan 1.3b$

Ma’aikatar Raya Karafa ta Najeriya ta rattaba hannu kan wata yarjejeniya da Premium Steel and Mines Limited (PSML) domin farfado da kamfanin karafa na Delta, da ke Ovwian-Aladja a Jihar Delta.

Masana sun yi gargadi kan amfani da man gyada ko yawu a matsayin man shafawa lokacin jima’i

Ya ce, “Ba za ka iya amfani da man gyada, man kayan lambu ko wasu irin wadannan sinadarai ba. Sai dai ana iya amfani da man shafawa mai ruwa, wanda shi ne abin da ya dace.”

Me ya sa za ku saka duk wanda kuka taɓa magana da shi sau ɗaya ko biyu a WhatsApp Group ɗin aurenku? – Mr....

Mr. Abdul Reacts ya ce matasan Najeriya da dama kan taimaka wa akalla biki ɗaya kusan kowane wata, ko da kuwa ba su da hali, abin da ya kwatanta da wani nau'in “haraji” da ake biya saboda kasancewa cikin abokan hulɗa.
spot_img

Labarai masu alaka

Sauran bangarori

spot_imgspot_img