Tinubu Zai Ci Zabe Kuma APC za ta ci gaba da mulkar Najeriya har bayan 2031 -inji Yari
Daga Wakiliya
Daraktan Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen APC, Sanata Abdul’Aziz Yari, ya ce yana da yaƙinin cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai sake lashe zaɓen shugaban ƙasa a 2027.
Yari ya kuma ce jam’iyyar APC za ta ci gaba da mulkin Najeriya har bayan shekarar 2031.
Ya bayyana hakan ne a filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe da ke Abuja, bayan dawowarsa daga wata tafiya da ya yi a ƙasar waje.
Magoya bayan APC ne suka tarbe shi a filin jirgin, inda suka yi masa addu’ar samun nasara a sabon aikin da aka ba shi na tabbatar da sake zaɓen Shugaba Tinubu.
Yari ya ce duk da kalubalen da gwamnatin Tinubu ke fuskanta, yana ganin ayyukan gwamnatin cikin shekaru uku da suka gabata za su taimaka wa APC wajen samun ƙarin wa’adi.
“Muna ganin shi a matsayin shugaban ƙasa a yau, kuma da yardar Allah zai kasance shugaban ƙasa a 2027,” in ji Yari.
Ya kuma tabbatar wa ’yan Najeriya cewa APC za ta cika alkawuran da ta ɗauka a lokacin yaƙin neman zaɓen 2023.
Ya ce jam’iyyar ta yi suna wajen cika alkawuranta, tare da yin addu’ar Allah Ya bai wa Shugaba Tinubu hikimar jagorantar ƙasar.
Kwamitin yaƙin neman zaɓen APC na 2027, wanda Shugaba Tinubu ke jagoranta, ya haɗa da Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima da Shugaban APC na ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda.
Gwamnan Imo kuma shugaban ƙungiyar gwamnonin APC, Sanata Hope Uzodimma, ne aka naɗa sakataren kwamitin, yayin da Abdul’Aziz Yari ya zama Darakta-Janar.
Sai dai tun bayan sanar da sunayen mambobin kwamitin, wasu ƴan siyasa da jam’iyyun adawa sun soki tsarin, musamman kan kasancewar wasu jami’an gwamnati da kuma mutanen da ke fuskantar zarge-zargen da ba a kammala bincikensu ba.
Duk da wannan suka, Yari ya ce yana fatan APC za ta ci gaba da kasancewa jam’iyyar da za ta jagoranci Najeriya bayan wa’adin mulkin Shugaba Tinubu na biyu.





