Gwamnatin Tarayya ta kulla yarjejeniyar farfado da Kamfanin Karafa na Delta cikin watanni 18 kan dala biliyan 1.3
Daga Wakiliya
Gwamnatin Tarayya ta kulla yarjejeniyar da za ta taimaka wajen farfado da Kamfanin Karafa na Delta, tare da alkawarin zuba jarin sama da dala biliyan 1.3 domin dawo da masana’antar bakin aiki.
Yarjejeniyar ta hada Ma’aikatar Raya Karafa ta Najeriya da kuma kamfanin Premium Steel and Mines Limited (PSML), mai kula da kamfanin karafan na Delta da ke Ovwian-Aladja a Jihar Delta.
A karkashin yarjejeniyar, PSML za ta zuba kudin wajen bincike da hako albarkatun kasa, gyara da inganta masana’antar, da kuma dawo da cikakken aikin samar da karafa.
Kamfanin ya ce yana shirin mayar da masana’antar cikin cikakken aiki tare da fara samar da karafa cikin watanni 18 zuwa 24, muddin aka samu isasshen karfen da ake bukata.
Ministan Raya Karafa, Prince Shuaibu Abubakar Audu, ya ce farfado da kamfanin na daga cikin kokarin gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na bunkasa masana’antu, samar da ayyukan yi da rage dogaro da karafan da ake shigowa da su daga kasashen waje.
Kamfanin Karafa na Delta, wanda aka kaddamar a shekarar 1982, yana da damar samar da tan miliyan guda na narkakken karafa a shekara, amma ya dade yana fuskantar matsalolin aiki.
Audu ya ce sabuwar yarjejeniyar za ta kuma taimaka wajen farfado da Kamfanin Hakar Karafa na Kasa, NIOMCO, da ke Itakpe a Jihar Kogi, domin tabbatar da samar da danyen karfen da masana’antar ke bukata.
Gwamnatin ta ce aikin na da damar samar da ayyukan yi kai tsaye kusan 5,000, da sama da 20,000 a kaikaice.
Ana kuma sa ran aikin zai taimaka wa Najeriya wajen cimma burinta na samar da tan miliyan 10 na narkakken karafa a shekara nan da 2030, tare da bunkasa sufurin kaya ta jirgin kasa da ruwa.
Ministan ya ce gwamnati na sa ran yarjejeniyar za ta haifar da gyaran masana’antar, ci gaban hakar ma’adinai da fara samar da karafa cikin wa’adin watanni 18 zuwa 24 da aka tsara.
Gwamnatin Tarayya ta ce farfado da masana’antar na daga cikin matakan da take dauka domin karfafa masana’antun cikin gida da rage dogaron Najeriya kan karafan da ake shigowa da su daga kasashen waje.




