Atiku: Da kyar Tinubu ya amince da Osinbajo a matsayin mataimakin Buhari
Daga Wakiliya
Tsohon Mataimakin Shugaban Najeriya, Atiku Abubakar, ya ce da kyar Bola Ahmed Tinubu ya amince da a zaɓi Farfesa Yemi Osinbajo a matsayin abokin takarar Muhammadu Buhari a zaɓen shugaban ƙasa na 2015.
Atiku ya ce bayan Buhari ya sauya ra’ayinsa kan zaɓen ɗan takarar mataimaki Musulmi, Tinubu ya nace cewa a zaɓi matarsa, Oluremi Tinubu, a matsayin mataimakiyar Buhari.
Ya ce sai da aka yi shiga tsakani da tattaunawa da dama kafin daga bisani aka samu Tinubu ya amince da saka sunan Osinbajo.
“Da kyar aka kai ga Osinbajo,” in ji Atiku.
Atiku ya bayyana hakan ne a wata hira, inda ya kuma ce lokacin da Buhari ya nemi goyon bayansa bayan taron APC na 2014, ya sharɗanta masa cewa kada ya tsaya da tikitin Musulmi da Musulmi.





