Bai kamata addini ya zama ma’aunin zaɓe ba domin a tsarin dimokuraɗiyyar Najeriya, tikitin Musulmi da Musulmi, Kirista da Kirista, Musulmi da Kirista ko Kirista da Musulmi duk siyasa ce kawai -Sheikh Daurawa
Daga Wakiliya
Fitaccen malamin addinin Musulunci daga Kano, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, ya ce bai kamata a rika kallon zaɓe a Najeriya a matsayin wani abu da addini zai zama ma’auninsa ba.
Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, wanda ke jagorantar hukumar Hisbah ta Kano, ya bayyana cewa a tsarin dimokuraɗiyya, tikitin Musulmi da Musulmi, Kirista da Kirista, Musulmi da Kirista ko Kirista da Musulmi duk siyasa ce kawai.
A wata hira da DW Hausa, Sheikh Daurawa ya ce ya kamata ’yan Najeriya su fi duba abin da ɗan takara yake yi da kuma abin da zai yi idan aka zaɓe shi, maimakon mayar da hankali kan addininsa.
Ya ce: “Idan Musulmi da Musulmi suka yi takara, ko Kirista da Kirista, ko Musulmi da Kirista, ko Kirista da Musulmi, duk abu ɗaya ne. Siyasa ce.”
Sheikh Daurawa ya kuma ce tsarin mulkin Najeriya da dimokuraɗiyyar ƙasar ba su ginu a kan Musulunci ko Kiristanci ba.
Ya ce da a ce Najeriya tana tafiyar da mulkin Shari’a yadda Alƙur’ani da koyarwar Annabi Muhammad (SAW) suka tanada, to Musulmi ne kaɗai za su iya neman shugabanci.
Sai dai ya ce a tsarin da ake ciki yanzu, bai kamata addini ya zama ma’aunin zaɓen ɗan takara ba.
Malamin ya ce ’yan Najeriya suna da hankali da za su iya zaɓar mutumin da suke ganin ya dace da su, ko da kuwa tikitin yana tsakanin Musulmi da Musulmi ne ko Kirista da Kirista.
Ya ƙara da cewa babu wata jam’iyya da hukumar zaɓe ta INEC ta yi wa rajista a matsayin jam’iyyar Musulmi ko Kirista da ke da tsarin gudanarwa bisa wannan akida.
Game da malaman addini da ke shiga siyasar jam’iyya, Sheikh Daurawa ya yi gargaɗin cewa duk malamin da ya shiga takarar jam’iyya ya kamata ya kasance cikin shirin rasa irin mutuncin da yake samu daga kowane ɓangare a matsayinsa na malami.
Ya ba da misalin tsohon mataimakin shugaban Najeriya, Farfesa Yemi Osinbajo, wanda ya shiga siyasar jam’iyya, yana mai cewa idan malami ya ɗauki tutar wata jam’iyya, sauran jam’iyyun za su iya kallonsa a matsayin ɗan siyasa.
Sheikh Daurawa ya kuma buƙaci ’yan siyasa da magoya bayansu su guji amfani da ƙwayoyi da makamai wajen yaƙin neman zaɓe, tare da daina zagin abokan hamayya da ɓata musu suna.
Ya ce ya kamata ’yan Najeriya su zaɓi ’yan takara bisa cancanta da abin da za su iya yi wa ƙasa.
Ya kuma bayyana cewa hukumar Hisbah na shirin shirya wani taro da masu magana da yawun jam’iyyun siyasa domin wayar da kansu kan yadda za su riƙa amfani da kalmomi cikin mutunci yayin kamfen.




