Labarai

Kujerar Gbajabiamila Ta Fara Rawa, ICPC Ta Gayyace Shi Kan Badakalar Hukumar Bogi Ta PFIPC

Binciken ya biyo bayan umarnin da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bayar a ranar 2 ga Yuli, inda ya umarci ICPC ta gudanar da cikakken bincike kan badakalar PFIPC tare da gabatar da rahoto cikin kwanaki 30.

Gwamna Bala Ya Nemi Tinubu Ya Saka Karatun Larabci Cikin Manhajar Ilimin Najeriya

Bala Mohammed Ya Bukaci A Saka Karatun Larabci Cikin Manhajar Ilimin Najeriya

Wajibi Ne Duk Ɗan Kaduna Ya Zaɓi Tinubu a 2027 Saboda Ayyukan Da Ya Kawo Jihar -inji Uba Sani

Hakazalika, gwamnan ya yi kira ga al'ummar Zariya su sake zaɓen Kakakin Majalisar Wakilai, Tajudeen Abbas, tare da goyon bayan 'yan takarar jam'iyyar APC a zaɓe mai zuwa.

Majalisa ta amince da tarar dubu N50,000 kan masu wa’azi da talla a cikin motocin haya

A cewar Majalisar Dattawa, gyaran dokar na da nufin karfafa aiwatar da dokokin hanya, rage hadurran mota da kuma inganta tsaron matafiya a fadin Najeriya.

Shettima ya bukaci ‘yan Najeriya su koma gona domin farfado da tattalin arziki

Ya ce noma ya taba zama abin da ya ba miliyoyin 'yan Najeriya damar samun abin dogaro da kai, yana mai kira ga gwamnati, masu zuba jari da matasa su kara mayar da hankali kan bunkasa bangaren.

Jagoranci ba na masu tausayi ko son faranta wa kowa rai ba bane – Shettima

"Jagoranci na nufin daukar matakai masu wahala. Kuma jagoranci ba na mutane masu son faranta wa kowa rai ba. Irin wadannan mutane su fi dacewa da sayar da cakulan ko ice cream."

Haɗakar Obi da Kwankwaso na fuskantar ƙalubale – Buba Galadima

Ya kuma yi kira ga 'yan Najeriya da kada su ɗora wa Peter Obi alhakin juyin mulkin soja na shekarar 1966, yana mai cewa Obi ba shi da wata alaƙa da abin da ya faru a lokacin.

Majalisar Dattawa Ta Sake Yin Watsi da Bukatar Neman Ta Binciki Batun Hukumar Bogi Ta PFIPC

Sanata Suleiman Kawu ne ya sake gabatar da bukatar a zaman majalisar na ranar Laraba, bayan makamanciyar bukata da ya gabatar a makon da ya gabata ta fadi.

MACRON ZAI ZIYARCI NAJERIYA: Shugaban Faransa Zai Zo Domin Ƙarfafa Dangantaka da Tinubu

Ya kuma ce Faransa da Najeriya na haɗin gwiwa a fannoni da dama, ciki har da noma, samar da wadataccen abinci, bunƙasa tattalin arziki, da yaƙi da ta'addanci a yankin.

Gwamnatin Tarayya Za Ta Ƙaddamar da Mafi Ƙarancin Fansho da Kulawar Lafiya Kyauta ga Masu Ritaya

Omolola ta bayyana cewa kadarorin fansho sun ƙaru daga Naira tiriliyan 20.79 zuwa Naira tiriliyan 31.48, yayin da aka samu sabbin masu bada gudummawar fansho sama da 938,229 cikin shekaru biyu.
- Advertisement -spot_img

DA DUMI-DUMI

Gwamnatin Najeriya za ta fara biyan tsoffin ma’aikatan Nigeria Airways Naira biliyan 18

Sai dai ya bayyana cewa gwamnati za ta biya kuɗin da aka tantance kuma aka tabbatar da shi, ba tare da ƙarin kuɗin da ya dace da hauhawar farashi na tsawon shekaru 20 ba.
- Advertisement -spot_img