Majalisa ta amince da tarar dubu N50,000 kan masu wa’azi da talla a cikin motocin haya

DA DUMI-DUMI

Daga Wakiliya

Majalisar Dattawan Najeriya ta amince da kudirin gyaran dokar Hukumar Kiyaye Haddura ta Kasa (FRSC), wanda ya tanadi karin hukunci ga masu karya dokokin hanya, ciki har da tarar N50,000 ga duk wanda aka samu da laifin yin talla, kasuwanci ko wa’azi a cikin motocin haya.

Kudirin, wanda aka tura domin amincewar Shugaban Kasa, ya kuma tanadi tarar N50,000, daurin wata shida ko duka biyun ga direbobin da suka ki ba jami’an FRSC hadin kai yayin gwajin shan barasa da ake yi idan akwai dalilin zargi.

Haka kuma, kudirin ya kara tarar tuki cikin maye ko bayan amfani da miyagun kwayoyi daga N5,000 zuwa N100,000, tare da yiwuwar daurin shekaru biyu ko kuma tara da dauri gaba daya.

Sauran sabbin hukuncin sun hada da karin tarar karya dokokin fitilun hanya, alamomin hanya da kuma gudun wuce ka’ida zuwa N100,000. Haka kuma, tuki cikin ganganci zai jawo tarar N100,000, daurin shekaru biyu ko duka biyun.

A cewar Majalisar Dattawa, gyaran dokar na da nufin karfafa aiwatar da dokokin hanya, rage hadurran mota da kuma inganta tsaron matafiya a fadin Najeriya.

- Advertisement -spot_img

Leave a Reply

- Advertisement -spot_img
Za ku so wadannan

Gwamnatin Najeriya za ta fara biyan tsoffin ma’aikatan Nigeria Airways Naira biliyan 18

Sai dai ya bayyana cewa gwamnati za ta biya kuɗin da aka tantance kuma aka tabbatar da shi, ba tare da ƙarin kuɗin da ya dace da hauhawar farashi na tsawon shekaru 20 ba.
- Advertisement -spot_img

Labarai masu alaka

- Advertisement -spot_img