MACRON ZAI ZIYARCI NAJERIYA: Shugaban Faransa Zai Zo Domin Ƙarfafa Dangantaka da Tinubu

DA DUMI-DUMI

Daga Wakiliya

Shugaban ƙasar Faransa, Emmanuel Macron, ya sanar da shirinsa na gudanar da ziyarar aiki ta ƙasa zuwa Najeriya domin ƙara ƙarfafa dangantakar da ke tsakanin ƙasashen biyu.

Jakadan Faransa a Najeriya da ECOWAS, Marc Fonbaustier, ne ya bayyana hakan a Abuja yayin bikin Ranar Ƙasa ta Faransa, inda ya ce ziyarar za ta gudana ne shekaru biyu bayan ziyarar da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya kai birnin Paris.

A cewarsa, Macron da Tinubu za su duba irin ci gaban da aka samu a yarjejeniyoyin haɗin gwiwar da suka cimma, tare da tsara sabbin manufofi da za su amfanar da ƙasashen biyu nan gaba.

Fonbaustier ya ce dangantakar Faransa da Najeriya ta ginu ne kan daidaito, mutunta juna da rashin tsoma baki cikin harkokin cikin gida, yana mai jaddada cewa ƙasashen biyu na aiki tare a matsayin abokan hulɗa masu daidaito.

Ya kuma ce Faransa da Najeriya na haɗin gwiwa a fannoni da dama, ciki har da noma, samar da wadataccen abinci, bunƙasa tattalin arziki, da yaƙi da ta’addanci a yankin.

Jakadan ya ƙara da cewa Shugaba Macron ya taɓa shafe watanni shida a Najeriya yana ɗalibi shekaru 24 da suka gabata, abin da ya ce ya taimaka wajen gina fahimtarsa game da Afirka da manufofin Faransa a nahiyar.

Rahoton Wakiliya

- Advertisement -spot_img

Leave a Reply

- Advertisement -spot_img
Za ku so wadannan

Gwamnatin Najeriya za ta fara biyan tsoffin ma’aikatan Nigeria Airways Naira biliyan 18

Sai dai ya bayyana cewa gwamnati za ta biya kuɗin da aka tantance kuma aka tabbatar da shi, ba tare da ƙarin kuɗin da ya dace da hauhawar farashi na tsawon shekaru 20 ba.
- Advertisement -spot_img

Labarai masu alaka

- Advertisement -spot_img