Jagoranci ba na masu tausayi ko son faranta wa kowa rai ba bane – Shettima

DA DUMI-DUMI

Daga Wakiliya

Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima, ya ce jagoranci na gaskiya yana bukatar jajircewa da daukar matakai masu wahala domin ci gaban kasa, ba wai neman farin jini a idon jama’a ba.

Shettima ya bayyana haka ne ranar Laraba yayin gabatar da jawabin bude taron noma da zuba jari, Niger Delta Agricultural Development and Investment Summit da aka gudanar a Abuja.

Ya yabawa Shugaban Rwanda, Paul Kagame, amma ya ce bai dace a rika kwatanta Najeriya da kasashe masu karancin yawan jama’a ba.

A cewarsa, yawan al’ummar Najeriya da bambancin da ke tsakaninsu na sa shugabancin kasar ya fi rikitarwa fiye da na kasashe irin su Rwanda, Botswana da Seychelles.

Da yake karin haske kan ma’anar shugabanci, Shettima ya ce:

“Jagoranci na nufin daukar matakai masu wahala. Kuma jagoranci ba na mutane masu raunin tausayi ko son faranta wa kowa rai ba ne. Irin wadannan mutane sun fi dacewa da sayar da cakulan ko ice cream.”

- Advertisement -spot_img

Leave a Reply

- Advertisement -spot_img
Za ku so wadannan

Gwamnatin Najeriya za ta fara biyan tsoffin ma’aikatan Nigeria Airways Naira biliyan 18

Sai dai ya bayyana cewa gwamnati za ta biya kuɗin da aka tantance kuma aka tabbatar da shi, ba tare da ƙarin kuɗin da ya dace da hauhawar farashi na tsawon shekaru 20 ba.
- Advertisement -spot_img

Labarai masu alaka

- Advertisement -spot_img