Haɗakar Obi da Kwankwaso na fuskantar ƙalubale – Buba Galadima

DA DUMI-DUMI

Daga Wakiliya
Jigo a jam’iyyar Nigeria Democratic Co

ngress (NDC), Buba Galadima, ya amince cewa ana fuskantar wasu ƙalubale wajen yunƙurin samar da haɗakar takarar shugaban ƙasa tsakanin Peter Obi da Rabiu Musa Kwankwaso.

Galadima ya bayyana haka a shirin Prime Time na gidan talabijin na Arise TV, inda ya ce duk da matsalolin da ake fuskanta, ba su kai matsayin da ba za a iya magance su ba.

“Muna da matsaloli da dama, amma ba matsalolin da ba za a iya shawo kansu ba ne. Za mu shawo kansu,” in ji Galadima.

Ya kuma yi kira ga ‘yan Najeriya da kada su ɗora wa Peter Obi alhakin juyin mulkin soja na shekarar 1966, yana mai cewa Obi ba shi da wata alaƙa da abin da ya faru a lokacin.

A cewarsa, bai dace a riƙa hukunta mutane saboda abubuwan da wasu suka aikata ba, yana mai jaddada cewa haɗin kan ƙasa zai samu ne idan aka daina riƙe ƙiyayyar tarihi.

Galadima ya kawo misalin marigayi Chukwuemeka Odumegwu Ojukwu, wanda bayan yaƙin basasa aka yi masa afuwa, sannan ya dawo ya shiga harkokin siyasar Najeriya.

Ya kuma ce idan ana magana kan rikicin shekarar 1966, ya kamata a tuna cewa ba shugabannin Arewa kaɗai suka rasa rayukansu ba, domin ‘yan kabilar Igbo ma sun yi asara mai yawa.

A ƙarshe, Galadima ya jaddada cewa sulhu da tattaunawa ne hanya mafi dacewa wajen rage rabuwar kai da kuma gina haɗin kan Najeriya.

- Advertisement -spot_img

Leave a Reply

- Advertisement -spot_img
Za ku so wadannan

Gwamnatin Najeriya za ta fara biyan tsoffin ma’aikatan Nigeria Airways Naira biliyan 18

Sai dai ya bayyana cewa gwamnati za ta biya kuɗin da aka tantance kuma aka tabbatar da shi, ba tare da ƙarin kuɗin da ya dace da hauhawar farashi na tsawon shekaru 20 ba.
- Advertisement -spot_img

Labarai masu alaka

- Advertisement -spot_img