Kujerar Gbajabiamila Ta Fara Rawa, ICPC Ta Gayyace Shi Kan Badakalar Hukumar Bogi Ta PFIPC

DA DUMI-DUMI

Daga Wakiliya

Alamu na nuna cewa kujerar Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa, Femi Gbajabiamila, ta fara shiga matsin lamba bayan Hukumar ICPC ta gayyace shi domin amsa tambayoyi kan zargin da ya shafi wata hukuma da ake kira Presidential Foreign Investment Promotion Council (PFIPC), wadda gwamnatin tarayya ta bayyana a matsayin hukuma ta bogi.

Gbajabiamila ya isa hedikwatar ICPC da ke Abuja a ranar Litinin, inda ya ba masu bincike bayanai kan zargin da ake yi wa hukumar PFIPC. Lauyansa, Jiti Ogunye, ya ce ya amsa dukkan tambayoyin da aka yi masa cikin cikakken haɗin kai, sannan ya koma bakin aikinsa bayan kammala zaman.

Binciken ya biyo bayan umarnin da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bayar a ranar 2 ga Yuli, inda ya umarci ICPC ta gudanar da cikakken bincike kan badakalar PFIPC tare da gabatar da rahoto cikin kwanaki 30.

Ko da yake ICPC ba ta zargi Gbajabiamila da aikata wani laifi ba a wannan mataki, gayyatarsa domin amsa tambayoyi ya nuna cewa binciken ya shiga wani sabon salo, yayin da ake ci gaba da bankado yadda aka gudanar da harkokin hukumar da gwamnati ta ce ba ta da sahihancin doka.

- Advertisement -spot_img

Leave a Reply

- Advertisement -spot_img
Za ku so wadannan

Gwamnatin Najeriya za ta fara biyan tsoffin ma’aikatan Nigeria Airways Naira biliyan 18

Sai dai ya bayyana cewa gwamnati za ta biya kuɗin da aka tantance kuma aka tabbatar da shi, ba tare da ƙarin kuɗin da ya dace da hauhawar farashi na tsawon shekaru 20 ba.
- Advertisement -spot_img

Labarai masu alaka

- Advertisement -spot_img