Gwamna Bala Ya Nemi Tinubu Ya Saka Karatun Larabci Cikin Manhajar Ilimin Najeriya

DA DUMI-DUMI

Daga Wakiliya

Gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed, ya bukaci Gwamnatin Tarayya ta haɗa karatun Larabci cikin manhajar ilimin Najeriya domin bai wa waɗanda suka yi karatu a ƙasashen Larabawa cikakkiyar damar a amince da takardun karatunsu kamar sauran masu digiri.

Bala Mohammed ya bayyana hakan ne yayin da ya karɓi baƙuncin tawagar ‘yan kasuwar Saudiyya da shugabannin ɗaliban Najeriya da ke karatu a jami’o’in Saudiyya, ƙarƙashin jagorancin Daraktan Cibiyar Nazarin Sunnah a Afirka, Dakta Shuaibu Abubakar Idris, a Fadar Gwamnatin Bauchi.

Gwamnan ya nuna damuwa kan abin da ya kira raguwar kulawa da gadon ilimin Larabci a Arewacin Najeriya, yana mai cewa yankin ya daɗe yana da alaƙa ta ilimi, addini da al’adu da ƙasashen Larabawa.

Ya kuma yi kira da a farfaɗo da tsohuwar Kwalejin Larabci ta Alkaleri, wadda ya ce ta taɓa yin fice amma aka yi watsi da ita a gwamnatocin da suka gabata.

A nasa jawabin, Dakta Shuaibu Abubakar Idris ya ce sun kai ziyarar ne domin gabatar da wasu ‘yan kasuwar Saudiyya masu sha’awar zuba jari a Jihar Bauchi, tare da bayyana ayyukan cibiyar da kuma irin tallafin da take bai wa ɗaliban Bauchi da ke karatu a Saudiyya.

A nasu ɓangaren, wakilan ɗaliban Najeriya da ke karatu a Saudiyya sun gode wa Bala Mohammed bisa goyon bayan da yake ba su, tare da alƙawarin amfani da ilimi da ƙwarewar da suka samu wajen bunƙasa Bauchi da Najeriya bayan kammala karatunsu.

- Advertisement -spot_img

Leave a Reply

- Advertisement -spot_img
Za ku so wadannan

Gwamnatin Najeriya za ta fara biyan tsoffin ma’aikatan Nigeria Airways Naira biliyan 18

Sai dai ya bayyana cewa gwamnati za ta biya kuɗin da aka tantance kuma aka tabbatar da shi, ba tare da ƙarin kuɗin da ya dace da hauhawar farashi na tsawon shekaru 20 ba.
- Advertisement -spot_img

Labarai masu alaka

- Advertisement -spot_img