Daga Wakiliya
Gwamnatin Tarayya ta sanar da cewa cikin watanni uku masu zuwa za ta ƙaddamar da sabbin tsare-tsaren da za su inganta rayuwar masu ritaya, ciki har da tabbatar da mafi ƙarancin kuɗin fansho da kuma samar da kulawar lafiya kyauta ga tsofaffin masu fansho marasa ƙarfi.
Darakta Janar ta Hukumar Kula da Fansho ta Ƙasa (PenCom), Misis Omolola Oloworaran, ce ta bayyana hakan yayin taron manema labarai da ta gudanar a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja, inda ta yi bayanin irin nasarorin da hukumar ta samu cikin shekaru biyu da suka gabata.
Ta ce shirin Minimum Pension Guarantee zai tabbatar da cewa babu mai fansho da zai riƙa karɓar kuɗin da bai kai mafi ƙarancin adadin da gwamnati ta tanada ba. Haka kuma, shirin PenCare zai bai wa tsofaffin masu ritaya marasa ƙarfi damar samun kulawar lafiya kyauta domin rage musu wahalhalun rayuwa bayan ritaya.
A cewarta, gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta amince da fitar da Naira biliyan 758, lamarin da ya taimaka wajen warware basussukan fansho da suka shafe sama da shekaru 20 tare da ƙara yawan kuɗin fanshon masu ritaya da ke ƙarƙashin tsarin Contributory Pension Scheme (CPS).
Omolola ta bayyana cewa kadarorin fansho sun ƙaru daga Naira tiriliyan 20.79 zuwa Naira tiriliyan 31.48, yayin da aka samu sabbin masu bada gudummawar fansho sama da 938,229 cikin shekaru biyu.
Ta kuma ce yawan kuɗin fansho da ake biya kowane wata ya ƙaru da kashi 22%, daga Naira biliyan 12.2 zuwa Naira biliyan 14.9, yayin da gwamnati ta amince da ƙarin N32,000 ga duk masu ritaya da suka cancanta daga ma’aikatun gwamnatin tarayya da suka yi ritaya kafin 29 ga Yuli, 2024.
Har ila yau, ta ce tsofaffin masu fansho na NSITF da suka shafe shekaru 20 ba tare da sake duba fanshonsu ba, yanzu suna karɓar N206,000 duk wata, fiye da ninki goma na abin da suke samu a baya, tare da biyan dukkan bashin da ake binsu.
Daraktar Janar ɗin ta ƙara da cewa PenCom na faɗaɗa tsarin fansho domin ya haɗa da masu sana’o’in hannu, ‘yan kasuwa, direbobi, manoma da sauran ma’aikatan ɓangaren masu zaman kansu ta hanyar Personal Pension Plan, tare da samar da Accredited Pension Agents a faɗin ƙasar domin sauƙaƙa rajista da ƙara samar da ayyukan yi ga matasa.
Ta tabbatar da cewa duk waɗannan matakai na daga cikin manufofin gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na tabbatar da cewa duk wani ɗan Najeriya da ya yi aiki na tsawon shekaru ya samu rayuwar ritaya cikin mutunci, walwala da kariya.





