Shettima ya bukaci ‘yan Najeriya su koma gona domin farfado da tattalin arziki

DA DUMI-DUMI

Daga Wakiliya

Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima, ya bukaci ‘yan Najeriya su sake rungumar harkar noma, yana mai cewa ita ce ta kafa tubalin tattalin arzikin kasar kuma har yanzu tana da muhimmiyar rawa wajen samar da ayyukan yi da bunkasa arziki.

Shettima ya bayyana haka ne a ranar Laraba yayin jawabin bude taron Niger Delta Agricultural Development and Investment Summit da aka gudanar a Abuja.

A cewarsa, Najeriya ta fara ne a matsayin kasa mai dogaro da noma, inda ya jaddada cewa lokaci ya yi da za a dawo da martabar wannan fanni domin karfafa tattalin arziki da tabbatar da wadatar abinci.

Ya ce noma ya taba zama abin da ya ba miliyoyin ‘yan Najeriya damar samun abin dogaro da kai, yana mai kira ga gwamnati, masu zuba jari da matasa su kara mayar da hankali kan bunkasa bangaren.

Kalaman Shettima na zuwa ne yayin da Gwamnatin Tarayya ta kaddamar da wani asusun zuba jari na dala miliyan 500 domin bunkasa noma a yankin Neja Delta tare da karfafa samar da abinci da jawo masu zuba jari.

- Advertisement -spot_img

Leave a Reply

- Advertisement -spot_img
Za ku so wadannan

Gwamnatin Najeriya za ta fara biyan tsoffin ma’aikatan Nigeria Airways Naira biliyan 18

Sai dai ya bayyana cewa gwamnati za ta biya kuɗin da aka tantance kuma aka tabbatar da shi, ba tare da ƙarin kuɗin da ya dace da hauhawar farashi na tsawon shekaru 20 ba.
- Advertisement -spot_img

Labarai masu alaka

- Advertisement -spot_img