Wajibi Ne Duk Ɗan Kaduna Ya Zaɓi Tinubu a 2027 Saboda Ayyukan Da Ya Kawo Jihar -inji Uba Sani

Daga Wakiliya

Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya buƙaci al’ummar jihar su bai wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu kashi 98 cikin 100 na kuri’unsu a zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2027.

Uba Sani ya bayyana hakan ne a ranar Asabar yayin ƙaddamar da ayyukan tituna guda 11 a ƙananan hukumomin Zariya da Sabon Gari. Ya ce Shugaba Tinubu ya nuna goyon baya sosai ga ayyukan raya ƙasa a Kaduna, musamman gina tituna da sauran manyan ayyukan more rayuwa.

Gwamnan ya ce gwamnatin tarayya ta kuma zaɓi Kaduna da Legas ne kaɗai domin aiwatar da aikin layin dogo na cikin birni (Light Rail), inda ya bayyana cewa aikin na Kaduna mai darajar tiriliyan N1 zai fara cikin watanni biyu masu zuwa, bayan an riga an tura ‘yan kwangila wuraren aiki.

Ya kuma sanar da cewa za a yi bikin aza harsashin titin Mando zuwa Birnin Gwari cikin makon nan, yana mai cewa Shugaba Tinubu ya riga ya ware sama da biliyan N100 domin aikin.

Uba Sani ya ce irin waɗannan ayyuka sun sa ya zama wajibi al’ummar Kaduna su mayar da alherin da shugaban ƙasa ya yi musu ta hanyar sake zaɓensa a 2027.

Hakazalika, gwamnan ya yi kira ga al’ummar Zariya su sake zaɓen Kakakin Majalisar Wakilai, Tajudeen Abbas, tare da goyon bayan ‘yan takarar jam’iyyar APC a zaɓe mai zuwa.

A cewarsa, ayyukan tituna guda 11 da aka ƙaddamar a Zariya da Sabon Gari za a kammala su cikin watanni biyar, yayin da gwamnatinsa ta fara ayyukan tituna sama da 150 masu tsawon fiye da kilomita 1,355, inda yawancinsu tuni aka kammala.

DA DUMI-DUMI

APC Za Ta Yi Amfani da Cikakken Ƙarfinta Domin Lashe Zaɓen 2027 – Nentawe Yilwatda

APC Za Ta Yi Amfani da Cikakken Ƙarfinta Domin Lashe Zaɓen 2027 Daga Kan Shugaban Kasa Har Kansila - Nentawe Yilwatda

Tsoron Talauci Na Jefa Mutane Da Dama Cikin Matsananciyar Damuwa – Masana

Tsoron Talauci Na Jefa Mutane Da Dama Cikin Matsananciyar Damuwa – Masana

Aliko Dangote Ya Yi Wasiyyar A Ware Kashi Ɗaya Bisa Uku Na Dukiyarsa, Kimanin Naira Tiriliyan 16, Domin Ayyukan Jin Ƙai — Halima Dangote

Aliko Dangote Ya Yi Wasiyyar A Ware Kashi Ɗaya Bisa Uku Na Dukiyarsa Domin Ayyukan Jin Ƙai — Halima Dangote

Kyaftin ɗin Super Falcons, Rashidat Ajibade, sanye da dankwali da aka rubuta “JESUS”

Kyaftin ɗin Super Falcons, Rashidat Ajibade, na bayyana bangaskiyarta ga Yesu a duk inda ta je.

Har Tsawon Wane Lokaci Za a Iya Ajiye Kifi a Firiza Kafin Ya Lalace?

Yawan Lokacin da Kifi Zai Iya Ɗauka a Firiza Kafin Ya Lalace

Kanun Labarai

Wani Magidanci a Kano Ya Kashe Wani Mutum Saboda Ya Yi Zargin Yana Neman Matarsa – Kiyawa

Wani Magidanci a Kano Ya Kashe Wani Mutum Saboda Ya Yi Zargin Yana Neman Matarsa – Kiyawa

Budurwa Ta Yanke Gaban Saurayinta a Kano Bayan Ya Shaida Mata Zai Auri Wata – Rundunar Yan Sanda

Budurwa Ta Yanke Gaban Saurayinta a Kano Bayan Ya Sanar da Ita Cewa Zai Auri Wata — Rundunar 'Yan Sanda

Mata Sun Fi Maza Cika Alƙawarin Biyan Bashi – Inji Rahoton Moniepoint

Moniepoint ta ce alkaluman sun nuna cewa, duk da matsalolin da mata ke fuskanta wajen samun rance saboda buƙatar jingina ko rashin tarihin bashi, suna daga cikin rukunin masu kasuwanci da suka fi nuna amana wajen biyan bashin da suka karɓa.
spot_img

Labarai masu alaka

Sauran bangarori

spot_imgspot_img