Majalisar Dattawa Ta Sake Yin Watsi da Bukatar Neman Ta Binciki Batun Hukumar Bogi Ta PFIPC

DA DUMI-DUMI

Daga Wakiliya

Majalisar Dattawa ta sake yin watsi da kudirin neman gudanar da bincike mai zaman kansa kan takaddamar da ta shafi Adeniyi Adeyemi, wanda ake zargi da gabatar da kansa a matsayin Darakta Janar na Presidential Economic Advisory Council/Presidential Foreign Investment Promotion Council (PEAC/PFIPC).

Sanata Suleiman Kawu ne ya sake gabatar da bukatar a zaman majalisar na ranar Laraba, bayan makamanciyar bukata da ya gabatar a makon da ya gabata bata samu shiga ba.

Sai dai Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya yi watsi da kudirin, yana mai cewa batun na gaban kotu, sannan Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya riga ya umarci ICPC ta gudanar da bincike, don haka bai dace majalisar ta shiga lamarin ba a wannan lokaci.

Duk da haka, Sanata Suleiman Kawu ya ce kundin tsarin mulki ya bai wa Majalisar Dokoki ikon sa ido kan ayyukan gwamnati, ko da kuwa bangaren zartarwa ya fara daukar mataki.

A halin yanzu, Babbar Kotun Tarayya ta bayar da umarnin kamo Adeniyi Adeyemi bayan ya kasa bayyana domin fuskantar tuhume-tuhume takwas da suka hada da zargin jabun takardu, damfara da kuma yin kage da mukami.

Gwamnatin Tarayya ta zarge shi da kirkirar takardar nadin mukami da aka ce Shugaba Tinubu ya bayar tare da sa hannun Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa, Femi Gbajabiamila, tare da amfani da takardun bogi wajen neman ofis, bude asusun banki da kuma neman amincewar hukumomin gwamnati.

Tun da farko, Adeniyi Adeyemi ya musanta dukkan zarge-zargen da ake masa, yana mai cewa a bar shari’a ta bi hanyarta.

Rahoton Wakiliya | Muryar Arewa a Duniya

- Advertisement -spot_img

Leave a Reply

- Advertisement -spot_img
Za ku so wadannan

Gwamnatin Najeriya za ta fara biyan tsoffin ma’aikatan Nigeria Airways Naira biliyan 18

Sai dai ya bayyana cewa gwamnati za ta biya kuɗin da aka tantance kuma aka tabbatar da shi, ba tare da ƙarin kuɗin da ya dace da hauhawar farashi na tsawon shekaru 20 ba.
- Advertisement -spot_img

Labarai masu alaka

- Advertisement -spot_img