Tinubu ya amince da yi wa ƙananan ‘yan kasuwa 250,000 rijistar CAC kyauta

DA DUMI-DUMI

Daga Wakiliya


Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya amince da yi wa ƙananan ‘yan kasuwa (MSMEs) 250,000 a faɗin Najeriya rijistar kasuwanci ta Hukumar CAC kyauta.

An sanar da hakan ne a ranar Asabar yayin bikin karrama ƙananan ‘yan kasuwa karo na 8 da aka gudanar a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja.

Gwamnatin Tarayya ta ce shirin zai taimaka wa ƙananan ‘yan kasuwa su yi rijistar kasuwancinsu ba tare da biyan kuɗin CAC ba, domin su samu damar cin gajiyar ayyukan bankuna da sauran shirye-shiryen gwamnati.

Baya ga rijistar kyauta, gwamnati za ta ba waɗanda suka ci gajiyar shirin horo kan yadda za su gudanar da kasuwancinsu domin ya bunƙasa.

An kuma bayyana cewa masu sha’awar cin gajiyar shirin za su shiga shafin SMEDAN domin cike bayanansu kafin a zaɓe su.

Shirin haɗin gwiwa ne tsakanin Hukumar CAC da Hukumar Bunƙasa Ƙananan da Matsakaitan Kasuwanci ta Najeriya (SMEDAN).

- Advertisement -spot_img

Leave a Reply

- Advertisement -spot_img
Za ku so wadannan

Gwamnatin Najeriya za ta fara biyan tsoffin ma’aikatan Nigeria Airways Naira biliyan 18

Sai dai ya bayyana cewa gwamnati za ta biya kuɗin da aka tantance kuma aka tabbatar da shi, ba tare da ƙarin kuɗin da ya dace da hauhawar farashi na tsawon shekaru 20 ba.
- Advertisement -spot_img

Labarai masu alaka

- Advertisement -spot_img