‘Duk Ɗan Sandan Da Ke Karɓar Kuɗi Daga Direbobi Barawo Ne’ – CP Ahmed Sanusi

DA DUMI-DUMI

Daga Wakiliya

Kwamishinan ‘Yan Sandan Babban Birnin Tarayya (FCT), Ahmed Sanusi, ya gargadi jami’an ‘yan sanda da su daina karɓar rashawa da kuma kwace kuɗi daga masu ababen hawa yayin gudanar da aikinsu.

Sanusi ya yi wannan gargaɗi ne a ranar Asabar yayin wani taron tsaro da aka gudanar domin duba yadda ake gudanar da ayyukan tsaro da kula da zirga-zirga a Abuja.

Ya ce rundunar ba za ta ƙara kare jami’an da ke cin zarafin direbobin Keke Napep da masu motoci ta hanyar karɓar kuɗi ba bisa ƙa’ida ba.

A cewarsa, koke-koken da jama’a ke yi kan cin zarafin jami’an ‘yan sanda sun yi yawa, don haka rundunar ta shirya tsabtace cikinta tare da hukunta duk masu hannu a irin waɗannan ayyuka.

“Ba ma son jin wani rahoto cewa ana karɓar kuɗi daga direbobin Keke Napep ko masu motoci a Abuja. Idan aka kama ka da hakan, kai ɓarawo ne.

“Ba za ka iya zama ɗan sanda kuma ɓarawo a lokaci guda ba. Dole ne ka zaɓi ɗaya,” in ji Sanusi.

- Advertisement -spot_img

Leave a Reply

- Advertisement -spot_img
Za ku so wadannan

Gwamnatin Najeriya za ta fara biyan tsoffin ma’aikatan Nigeria Airways Naira biliyan 18

Sai dai ya bayyana cewa gwamnati za ta biya kuɗin da aka tantance kuma aka tabbatar da shi, ba tare da ƙarin kuɗin da ya dace da hauhawar farashi na tsawon shekaru 20 ba.
- Advertisement -spot_img

Labarai masu alaka

- Advertisement -spot_img