Matuƙin jirgi ya kamu da farfaɗiya a sararin samaniya yana tsaka da tuka fasinjoji

DA DUMI-DUMI

Daga Wakiliya

Fasinjoji sun taimaka wajen dakile matuƙin jirgi bayan ya kamu da matsalar lafiya a sararin samaniya

Fasinjoji sun shiga tsakani domin taimakawa bayan matuƙin wani jirgin saman Air Canada ya kamu da matsalar lafiya yayin da jirgin ke tsaka da tafiya daga Newark na Amurka zuwa Halifax a ƙasar Canada.

Kamfanin Air Canada ya ce mataimakin matuƙin jirgin ne ya karɓi ragamar sarrafa jirgin tare da karkatar da shi zuwa Boston, inda aka sauka lafiya da fasinjoji 61 da ke cikinsa.

Wani fasinja, Rodney McDonald, ya ce ya fara zargin akwai matsala ne bayan jirgin ya riƙa karkacewa ba tare da alamar girgizar iska ba. Ya ce daga bisani ma’aikaciyar jirgi ta shiga ɗakin matuƙa kafin aka fito da kyaftin ɗin zuwa cikin jirgin.

McDonald ya ce shi da wasu fasinjoji sun taimaka wajen riƙe kyaftin ɗin, wanda ake zargin ya kamu da farfaɗiya, har na kusan mintuna 40 yayin da mataimakin matuƙin ke saukar da jirgin cikin aminci.

Haka kuma, wata ma’aikaciyar jinya da ke cikin jirgin ta taimaka wajen kula da lafiyar kyaftin ɗin har zuwa saukar jirgin.

An garzaya da matuƙin zuwa asibiti domin samun kulawa, yayin da Air Canada ta tabbatar da cewa an horar da matuƙan jiragen ta yadda za su iya saukar da jirgi cikin aminci ko da matuƙi ɗaya ne kawai ke aiki.

- Advertisement -spot_img

Leave a Reply

- Advertisement -spot_img
Za ku so wadannan

Shaharata a ƙauyukan Gombe ta fi abin da ake gani a kafafen sada zumunta’ – Pantami

Ya ce idan aka zaɓe shi, gwamnatinsa za ta fi mayar da hankali kan bunƙasa ilimi, samar da ayyukan yi da koyar da matasa sana’o’in zamani, maimakon dogaro da rabon kuɗi.
- Advertisement -spot_img

Labarai masu alaka

- Advertisement -spot_img