Sabuwar Dokar NIMC za ta ƙarfafa kariyar bayanan ƴan Najeriya – inji Tunji-Ojo

DA DUMI-DUMI

Daga Wakiliya


Ministan Harkokin Cikin Gida, Dakta Olubunmi Tunji-Ojo, ya ce sabuwar Dokar Hukumar Kula da Shaidar Ɗan Ƙasa (NIMC) ta shekarar 2026 za ta kawo sauyi mai girma wajen inganta tsarin tantance ƴan ƙasa da kuma kare bayanansu.

Dokar, wadda Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sanya wa hannu, ta soke tsohuwar dokar NIMC ta 2007, tare da samar da sabbin tanade-tanade da suka dace da zamani.

A cewar Tunji-Ojo, dokar za ta ƙara kariya ga bayanan sirri na ƴan Najeriya, ta sauƙaƙa samun ayyukan gwamnati da na kamfanoni ta hanyar amfani da shaidar dijital, tare da ƙarfafa tsaron mu’amalolin intanet.

Ya ce dokar ta kuma ba NIMC ikon jagorantar tsarin tantance sahihancin shaidar dijital a ƙasar, da kuma sauƙaƙa musayar bayanai tsakanin hukumomin gwamnati da masu zaman kansu cikin tsaro.

Ministan ya ƙara da cewa, ‘yan Najeriya ciki da wajen ƙasa za su amfana da sauƙin samun ayyukan tantance shaida, ingantacciyar kariyar bayanai, da kuma ƙarin amincewa da harkokin kasuwanci ta yanar gizo.

Tunji-Ojo ya bayyana cewa wannan ci gaba wani muhimmin mataki ne na cika burin gwamnatin Shugaba Tinubu na gina tattalin arzikin Najeriya da darajarsa za ta kai dala tiriliyan ɗaya.

- Advertisement -spot_img

Leave a Reply

- Advertisement -spot_img
Za ku so wadannan

Gwamnatin Najeriya za ta fara biyan tsoffin ma’aikatan Nigeria Airways Naira biliyan 18

Sai dai ya bayyana cewa gwamnati za ta biya kuɗin da aka tantance kuma aka tabbatar da shi, ba tare da ƙarin kuɗin da ya dace da hauhawar farashi na tsawon shekaru 20 ba.
- Advertisement -spot_img

Labarai masu alaka

- Advertisement -spot_img