Shugaban Serbia Zai Yi Murabus Bayan Zanga-Zanga Kan Mutuwar Mutum 16

DA DUMI-DUMI

Daga Wakiliya

Shugaban ƙasar Serbia, Aleksandar Vučić, ya bayyana cewa zai yi murabus cikin makonni masu zuwa, tare da ba da damar gudanar da zaɓen shugaban ƙasa da na ‘yan majalisa kafin wa’adinsu ya ƙare.

Vučić ya sanar da hakan ne yayin wani gangamin magoya bayansa a babban birnin ƙasar, Belgrade, bayan kusan watanni 18 ana gudanar da zanga-zangar adawa da gwamnatinsa ƙarƙashin jagorancin ɗalibai.

Zanga-zangar ta samo asali ne bayan rushewar rumfar tashar jirgin ƙasa a birnin Novi Sad a watan Nuwamban 2024, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutum 16. Masu zanga-zangar sun ce hatsarin ya nuna gazawar gwamnati wajen gudanar da ayyukan gine-gine da kuma yawaitar cin hanci da rashawa.

Ko da yake Vučić ya ce zai sauka daga kujerar shugaban ƙasa, masana na ganin hakan ba yana nufin zai fice daga siyasa ba, domin akwai yiwuwar ya sake neman kujerar Firaminista idan jam’iyyarsa ta lashe zaɓen.

A nasa bangaren, ‘yan adawa sun ce matakin da shugaban ya ɗauka na nufin ƙoƙarin dakile tasirin zanga-zangar da kuma ƙarfafa matsayin jam’iyyarsa kafin zaɓe.

- Advertisement -spot_img

Leave a Reply

- Advertisement -spot_img
Za ku so wadannan

Shaharata a ƙauyukan Gombe ta fi abin da ake gani a kafafen sada zumunta’ – Pantami

Ya ce idan aka zaɓe shi, gwamnatinsa za ta fi mayar da hankali kan bunƙasa ilimi, samar da ayyukan yi da koyar da matasa sana’o’in zamani, maimakon dogaro da rabon kuɗi.
- Advertisement -spot_img

Labarai masu alaka

- Advertisement -spot_img