An daina kashe mutane a Najeriya tun bayan da Sojojin Amurka suka kai hare-hare kasar -inj Trump

DA DUMI-DUMI

Daga Wakiliya

Shugaban Amurka, Donald Trump, ya ce matakan soji da ƙasarsa ta ɗauka sun taimaka wajen dakatar da kashe-kashen Kiristoci a Najeriya.

Trump ya bayyana haka ne yayin wani taro a birnin Washington, inda ya ce hare-haren da Amurka ta kai sun yi wa shugabannin masu tayar da kayar baya mummunar illa.

A cewarsa, an kashe dubban Kiristoci da suka haɗa da mata, yara da tsofaffi kafin matakan da Amurka ta ɗauka.

Ya kuma yi ikirarin cewa an kashe jagoran ƙungiyar da mataimakansa, lamarin da ya sa sauran mayaƙan suka ja da baya saboda tsoron ƙarin hare-haren Amurka.

Sai dai Trump bai bayyana cikakken bayani kan irin harin da ya ce Amurka ta kai a Najeriya ko lokacin da hakan ya faru ba.

- Advertisement -spot_img

Leave a Reply

- Advertisement -spot_img
Za ku so wadannan

Gwamnatin Najeriya za ta fara biyan tsoffin ma’aikatan Nigeria Airways Naira biliyan 18

Sai dai ya bayyana cewa gwamnati za ta biya kuɗin da aka tantance kuma aka tabbatar da shi, ba tare da ƙarin kuɗin da ya dace da hauhawar farashi na tsawon shekaru 20 ba.
- Advertisement -spot_img

Labarai masu alaka

- Advertisement -spot_img