Faɗuwar Farashin Ɗanyen Mai Kaɗai Ba Za Ta Rage Farashin Fetur ba -inji Masanin Tattalin Arziki

DA DUMI-DUMI

Daga Wakiliya

Farfesa Emeritus a fannin tattalin arzikin man fetur, Wumi Iledare, ya ce faɗuwar farashin ɗanyen mai a kasuwar duniya ba ta nufin farashin fetur zai sauka nan take a Najeriya.

Ya bayyana cewa masu shigo da ko sayar da fetur kan sayi haja ne tun lokacin da farashin ya yi tsada, don haka rage farashi cikin gaggawa na iya jefa su cikin asara tare da kawo cikas ga samar da mai.

A cewarsa, darajar dala kan naira na daga cikin manyan abubuwan da ke ƙayyade farashin fetur, saboda ana saye da dala. Don haka, ko da farashin ɗanyen mai ya faɗi, idan naira ba ta ƙarfi, farashin fetur ba zai sauka sosai ba.

Iledare ya kuma ce a ƙarƙashin dokar Petroleum Industry Act (PIA), kasuwa ce ke ƙayyade farashin fetur, ba umarnin gwamnati ba. Ya ƙara da cewa domin a samu sauƙin farashi mai ɗorewa, Najeriya na buƙatar ƙarfafa darajar naira, haɓaka tace mai a cikin gida, inganta sufuri da tabbatar da gasa mai inganci a kasuwa.

A halin yanzu, farashin litar fetur a Abuja na tsakanin N1,241 zuwa N1,305, duk da cewa matatar Dangote ta rage farashin sayar da fetur ga dillalai a kwanakin baya.

- Advertisement -spot_img

Leave a Reply

- Advertisement -spot_img
Za ku so wadannan

Gwamnatin Najeriya za ta fara biyan tsoffin ma’aikatan Nigeria Airways Naira biliyan 18

Sai dai ya bayyana cewa gwamnati za ta biya kuɗin da aka tantance kuma aka tabbatar da shi, ba tare da ƙarin kuɗin da ya dace da hauhawar farashi na tsawon shekaru 20 ba.
- Advertisement -spot_img

Labarai masu alaka

- Advertisement -spot_img