Majiyoyin sun kuma ce an gudanar da ɗaukar ma'aikatan ne a daidai lokacin da NNPCL ke aiwatar da shirin fitar da wasu tsofaffin ma'aikata daga aiki, lamarin da ya jawo damuwa kan yadda ake tafiyar da harkokin kamfanin.
Sanata Suleiman Kawu ne ya sake gabatar da bukatar a zaman majalisar na ranar Laraba, bayan makamanciyar bukata da ya gabatar a makon da ya gabata ta fadi.
Mahukuntan Mozambique sun tabbatar da kashe mutum biyu, tare da yin gargaɗin cewa akwai yiwuwar ƙarin hare-hare idan ba a dakile yaɗuwar wannan camfi ba.
Ya kuma ce Faransa da Najeriya na haɗin gwiwa a fannoni da dama, ciki har da noma, samar da wadataccen abinci, bunƙasa tattalin arziki, da yaƙi da ta'addanci a yankin.
Omolola ta bayyana cewa kadarorin fansho sun ƙaru daga Naira tiriliyan 20.79 zuwa Naira tiriliyan 31.48, yayin da aka samu sabbin masu bada gudummawar fansho sama da 938,229 cikin shekaru biyu.
A cewarsa, abin takaici ne yadda wasu gwamnoni ke nuna rashin ikon biyan mafi ƙarancin albashi ga ma'aikata, amma a lokaci guda suna kashe makudan kuɗaɗe wajen kula da jin daɗin alƙalai
Ya ce idan aka zaɓe shi, gwamnatinsa za ta fi mayar da hankali kan bunƙasa ilimi, samar da ayyukan yi da koyar da matasa sana’o’in zamani, maimakon dogaro da rabon kuɗi.