Daga Wakiliya
Dan takarar Gwamnan Jihar Gombe na jam’iyyar PDP, Farfesa Isa Ali Pantami, ya sake jan hankalin jama’a bayan ya kai ziyarar jaje Cocin ECWA da ke unguwar Federal Low-Cost a Gombe, wadda gobara ta yi wa ɓarna kwanakin baya.
A ziyarar da ya kai a safiyar Lahadi, Pantami ya wakilci jagoran PDP a jihar Gombe kuma Sanatan Gombe ta Arewa, Dr. Ibrahim Hassan Dankwambo, inda ya isar da saƙon ta’aziyya ga shugabanni da mambobin cocin.
Pantami, wanda ya bayyana cewa mazaunin yankin ne kuma maƙwabcin cocin, ya yi addu’ar Allah Ya maye musu da mafifici tare da jaddada haɗin kai da zaman lafiya tsakanin al’ummomi.
Ziyarar ta haifar da muhawara a tsakanin masu bibiyar siyasar Gombe, inda wasu ke ganin hakan na nuna sabon salon siyasar kusanci da kowane ɓangare na al’umma yayin da ake tunkarar zaɓen 2027.
Ko wannan wata alama ce ta sabon salo a siyasar Pantami? Kuma ina kuma za a ganshi a karo na gaba yayin da fafatawar siyasa ke ƙara zafi?





