Daga Wakiliya
Sabbin zarge-zarge sun taso kan Kamfanin Man Fetur na Ƙasa (NNPCL) bayan rahoton majiyar Wakiliya ya yi ikirarin cewa kamfanin ya ɗauki sabbin manyan ma’aikata a ɓoye ba tare da sanar da jama’a ko gudanar da buɗaɗɗen tsarin daukar aiki ba.
Rahoton ya ce an naɗa akalla mutane 15 a manyan muƙamai, inda mafi yawansu suka fito daga jihohin Kudu. Wasu majiyoyi sun yi zargin cewa hakan ya saɓa da ƙa’idar Federal Character, wadda ke tabbatar da daidaito wajen rabon mukamai.
Majiyoyin sun kuma ce an gudanar da ɗaukar ma’aikatan ne a daidai lokacin da NNPCL ke aiwatar da shirin fitar da wasu tsofaffin ma’aikata daga aiki, lamarin da ya jawo damuwa kan yadda ake tafiyar da harkokin kamfanin.
Sai dai har zuwa lokacin wallafa wannan rahoto, Babban Jami’in Hulɗa da Jama’a na NNPCL, Andrew Odeh, bai mayar da martani ba kan zarge-zargen.
Wakiliya ta lura cewa waɗannan zarge-zarge sun samo asali ne daga rahoton Daily Nigerian, kuma NNPCL ba ta fitar da wata sanarwa a hukumance da ke tabbatar ko ƙaryata ikirarin ba.





