Kotu ta kwace Jami’a, Gidan Rediyo da kadarori 46 da suka kai Naira Biliyan 213bn da aka alakanta su da Abubakar Malami

Daga Wakiliya

Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta ba da umarnin ƙwace kaddarori 48 da aka kiyasta darajarsu ta kai Naira biliyan 213bn da Hukumar EFCC ta ce suna da alaƙa da tsohon Babban Lauyan Tarayya kuma Ministan Shari’a, Abubakar Malami (SAN), tare da mayar da su mallakin Gwamnatin Tarayya.

Alƙaliya Joyce Abdulmalik ta yanke hukuncin ne bayan ta ce EFCC ta gabatar da hujjojin da suka nuna ana zargin an mallaki kaddarorin ne da kuɗaɗen da ba su fito daga halastattun hanyoyin samun kuɗi ba, yayin da waɗanda suka ƙalubalanci ƙwacen suka kasa nuna sahihin asalin kuɗaɗen da aka yi amfani da su wajen sayen su.

Daga cikin manyan kaddarorin da kotun ta umarci a ƙwace akwai Rayhaan University da rassa da gine-ginenta a Jihar Kebbi, Rayhaan Radio, Rayhaan Agro Allied Factory, Azbir Arena, da otal-otal, gidaje, filaye, shaguna da sauran kadarori a Abuja, Kano da Kebbi.

Tun a ranar 6 ga Janairu, 2026, kotu ta fara bayar da umarnin ƙwace kadarorin na wucin gadi. Bayan EFCC ta wallafa sanarwar a jaridu domin bai wa masu ruwa da tsaki damar kare kansu, Abubakar Malami da wasu mutum 14 da suka haɗa da ‘yan uwansa da abokan hulɗarsa sun garzaya kotu suna ƙalubalantar umarnin.

Sai dai a hukuncin ƙarshe da aka yanke a ranar Laraba, kotun ta ce masu ƙalubalantar ƙwacen sun kasa gabatar da hujjojin da za su tabbatar da cewa an sayi kadarorin ne da kuɗaɗen da aka samu ta halastacciyar hanya. Saboda haka, kotun ta tabbatar da ƙwace dukkan kaddarorin 48 tare da mayar da su mallakin Gwamnatin Tarayya.

Me zaku ce?

LIKE | SHARE & FOLLOW => Wakiliya
DUBA COMMENT SECTION⤵️

DA DUMI-DUMI

APC Za Ta Yi Amfani da Cikakken Ƙarfinta Domin Lashe Zaɓen 2027 – Nentawe Yilwatda

APC Za Ta Yi Amfani da Cikakken Ƙarfinta Domin Lashe Zaɓen 2027 Daga Kan Shugaban Kasa Har Kansila - Nentawe Yilwatda

Tsoron Talauci Na Jefa Mutane Da Dama Cikin Matsananciyar Damuwa – Masana

Tsoron Talauci Na Jefa Mutane Da Dama Cikin Matsananciyar Damuwa – Masana

Aliko Dangote Ya Yi Wasiyyar A Ware Kashi Ɗaya Bisa Uku Na Dukiyarsa, Kimanin Naira Tiriliyan 16, Domin Ayyukan Jin Ƙai — Halima Dangote

Aliko Dangote Ya Yi Wasiyyar A Ware Kashi Ɗaya Bisa Uku Na Dukiyarsa Domin Ayyukan Jin Ƙai — Halima Dangote

Kyaftin ɗin Super Falcons, Rashidat Ajibade, sanye da dankwali da aka rubuta “JESUS”

Kyaftin ɗin Super Falcons, Rashidat Ajibade, na bayyana bangaskiyarta ga Yesu a duk inda ta je.

Har Tsawon Wane Lokaci Za a Iya Ajiye Kifi a Firiza Kafin Ya Lalace?

Yawan Lokacin da Kifi Zai Iya Ɗauka a Firiza Kafin Ya Lalace

Kanun Labarai

Wani Magidanci a Kano Ya Kashe Wani Mutum Saboda Ya Yi Zargin Yana Neman Matarsa – Kiyawa

Wani Magidanci a Kano Ya Kashe Wani Mutum Saboda Ya Yi Zargin Yana Neman Matarsa – Kiyawa

Budurwa Ta Yanke Gaban Saurayinta a Kano Bayan Ya Shaida Mata Zai Auri Wata – Rundunar Yan Sanda

Budurwa Ta Yanke Gaban Saurayinta a Kano Bayan Ya Sanar da Ita Cewa Zai Auri Wata — Rundunar 'Yan Sanda

Mata Sun Fi Maza Cika Alƙawarin Biyan Bashi – Inji Rahoton Moniepoint

Moniepoint ta ce alkaluman sun nuna cewa, duk da matsalolin da mata ke fuskanta wajen samun rance saboda buƙatar jingina ko rashin tarihin bashi, suna daga cikin rukunin masu kasuwanci da suka fi nuna amana wajen biyan bashin da suka karɓa.
spot_img

Labarai masu alaka

Sauran bangarori

spot_imgspot_img