‘Ba Kuri’un Jama’a ‘Yan Siyasa Ke Bukata Ba, Alƙalai Suke Bukata’ – OdinkaluOdinkalu

DA DUMI-DUMI


Daga Wakiliya


Tsohon Shugaban Hukumar Kare Haƙƙin Dan Adam ta Ƙasa, Farfesa Chidi Odinkalu, ya yi ikirarin cewa a Najeriya, wasu ‘yan siyasa ba sa buƙatar kuri’un jama’a domin samun mulki, sai dai goyon bayan alƙalai.

Odinkalu ya ce hakan ne ya sa ake ganin wasu gwamnoni da manyan ‘yan siyasa suna gina gidaje, ba da motocin alfarma irin su Prado da Land Cruiser, tare da samar da wasu manyan alawus ga alƙalai.

A cewarsa, abin takaici ne yadda wasu gwamnoni ke nuna rashin ikon biyan mafi ƙarancin albashi ga ma’aikata, amma a lokaci guda suna kashe makudan kuɗaɗe wajen kula da jin daɗin alƙalai.

Sai dai Odinkalu bai gabatar da wata hujja da ke tabbatar da waɗannan zarge-zargen ba, kuma mutanen da ya ambata ba su mayar da martani kan kalaman nasa ba.

- Advertisement -spot_img

Leave a Reply

- Advertisement -spot_img
Za ku so wadannan

Gwamnatin Najeriya za ta fara biyan tsoffin ma’aikatan Nigeria Airways Naira biliyan 18

Sai dai ya bayyana cewa gwamnati za ta biya kuɗin da aka tantance kuma aka tabbatar da shi, ba tare da ƙarin kuɗin da ya dace da hauhawar farashi na tsawon shekaru 20 ba.
- Advertisement -spot_img

Labarai masu alaka

- Advertisement -spot_img