Sai da Lasisi: Gwamnatin Ghana Ta Haramta Nuna Fina-finan Najeriya a Tashoshin Talabijin din Kasar

DA DUMI-DUMI

Daga Wakiliya

Gwamnatin Ghana ta sanar da cewa za ta ɗauki mataki kan duk wata tashar talabijin da ke nuna fina-finan Najeriya ba tare da cikakken izini ba.

Mataimakin Shugaban Hukumar Kula da Masana’antar Fina-finai ta Ghana (NFA), James Gardiner, ya ce gwamnati na aiki tare da hukumomin sadarwa domin ƙirƙirar dokar da za ta soke lasisin duk tashoshin TV da suka karya ƙa’ida, kafin a tilasta musu sake neman sabbin lasisoshi.

James Gardiner ya bayyana hakan ne bayan wani furodusan fina-finai na Najeriya, Uchenna Mbunabo, ya zargi wasu tashoshin talabijin na Ghana da sauke fina-finan Nollywood daga YouTube tare da nuna su ba tare da izinin masu su ba.

A cewarsa, ana sa ran sabuwar dokar za ta fara aiki nan da shekarar 2027.

Tun da farko, fitattun jaruman Nollywood da suka haɗa da Bimbo Ademoye, Omoni Oboli, Mercy Johnson da Ruth Kadiri sun sha yin korafin cewa wasu tashoshin talabijin na Ghana na nuna fina-finansu ba tare da izini ba.

- Advertisement -spot_img

Leave a Reply

- Advertisement -spot_img
Za ku so wadannan

Gwamnatin Najeriya za ta fara biyan tsoffin ma’aikatan Nigeria Airways Naira biliyan 18

Sai dai ya bayyana cewa gwamnati za ta biya kuɗin da aka tantance kuma aka tabbatar da shi, ba tare da ƙarin kuɗin da ya dace da hauhawar farashi na tsawon shekaru 20 ba.
- Advertisement -spot_img

Labarai masu alaka

- Advertisement -spot_img