Na Yi Aure Tun Ban Gama Sakandare Ba; Yanzu Shekaru na 42, Yara na Uku Kuma Har Yanzu Ina da Aure” – inji Lubna Boƙararriya

DA DUMI-DUMI

Daga Wakiliya / Tsokaci daga Inuwa Muhammad Inuwa

Na kalli hirar da Usman Kabara yayi da fitacciyar yar TikTok mai hure wa mata kunne su boƙare wa mazajensu, Lubna Saleh Michika (Boƙararriya), shekarunta 42 an mata aure tun bata gama sikandire ba, tanada yara uku masu shekaru 21, 18 da 16 kuma har yanzu da aurenta.

Amma ku kalli irin content ɗinta a media na encouraging mata su boƙare su yi fito na fito da maza da sauransu, ita yanzu ko yanzu ta rasa aure ta gama cin ribar komai a cikin aure.

Tambayar shi ne ka taɓa ji Lubna ta kawo ƙarar mijinta media ko kun taɓa ji ta ba ku labarin yadda take gasa masa aya a hannu?

Amma Allah kaɗai ya san adadin matan da suka tasirantu da ideas da ra’ayoyinta, suna ganin cewa ta taɓa musu inda yake musu ciwo.

Ya kamata mu fahimta 95% of what we’re seeing online is fake, da yawan masu faɗa ko rubuta wasu abubuwan ba shi nw real life ɗin su ba.

- Advertisement -spot_img

Leave a Reply

- Advertisement -spot_img
Za ku so wadannan

Gwamnatin Najeriya za ta fara biyan tsoffin ma’aikatan Nigeria Airways Naira biliyan 18

Sai dai ya bayyana cewa gwamnati za ta biya kuɗin da aka tantance kuma aka tabbatar da shi, ba tare da ƙarin kuɗin da ya dace da hauhawar farashi na tsawon shekaru 20 ba.
- Advertisement -spot_img

Labarai masu alaka

- Advertisement -spot_img