Zenith Bank ta bayyana cewa bayanan da aka samu damar shiga sun haɗa da wasu adireshoshin imel (email) da kuma lambobin waya na wasu kwastomomi. Sai dai bankin ya ce har yanzu binciken yana gudana.
• Ka riƙa shan isasshen ruwa. • Ka yi barci na awa 7 zuwa 9 a kullum. • Ka gama cin abinci awa 2 zuwa 3 kafin kwanciya idan zai yiwu. • Idan yunwa ta taso da dare, ka zaɓi ɗan abin ci mai gina jiki maimakon kayan zaki ko abubuwan sha masu sukari.
"Ina so ku ƙara ƙaimi wajen tattara bayanan sirri. Kada ku tausaya wa kowa. Ko da ɗana ne yake da hannu a haƙar ma'adinai ba bisa ƙa'ida ba, ku ɗauki mataki a kansa," in ji gwamnan.
Ta ce ba talauci ko neman kuɗi ne ya sa ta bar Najeriya ba, sai dai abubuwan baƙin ciki da ta fuskanta bayan mutuwar 'ya'yanta biyu cikin ɗan gajeren lokaci.
Matakin ya zo ne sa'o'i kaɗan bayan Gwamnan Jihar Osun, Ademola Adeleke, ya zargi EFCC da shirin daskarar da asusun gwamnatin jihar da kuma na wasu manyan jami'an gwamnati gabanin zaɓen gwamnan jihar da za a gudanar ranar 15 ga Agusta
Oba Ogunronbi ya yi wannan kira ne yayin da ya karɓi Sarkin Hausawan Shasha, Alhaji Ilyasu Isah Kira, da shugabannin al'ummar Hausawa daga ƙananan hukumomi shida na Alimosho a fadarsa.
Tinubu ya kuma buƙaci jami'an sojin su ɗauki wannan ƙarin albashi a matsayin wata alama ta godiyar gwamnati bisa hidimar da suke yi wa ƙasa, yana mai bayyana fatan cewa tare za su yi nasara a kan masu neman tayar da zaune tsaye a Najeriya.
Ya ce idan aka zaɓe shi, gwamnatinsa za ta fi mayar da hankali kan bunƙasa ilimi, samar da ayyukan yi da koyar da matasa sana’o’in zamani, maimakon dogaro da rabon kuɗi.