Fiye da Mutum 1,000 Sun Amfana da Tallafin Naira miliyan ɗai-dai da Kayan Sana’o’i a Lagos
Daga Wakiliya
Fiye da mutum 1,000 mazauna ƙaramar hukumar Lagos Mainland sun amfana da tallafin kuɗi, kayan sana’a da kayan abinci yayin bikin cika shekara guda da hawan gwamnatin shugaban ƙaramar hukumar, Jibril Emilagba.
Tallafin ya haɗa da kuɗi, injinan ɗinki, firiza, injinan niƙa, injinan yin abin sha, murhun gas, tare da kayan abinci kamar shinkafa, doya, ƙwai da taliyar noodles.
Jibril Emilagba ya ce shirin na da nufin inganta rayuwar al’umma, tallafa wa ƙananan ‘yan kasuwa da rage radadin matsin tattalin arziki. Ya ce gwamnatinsa ta ci gaba da cika alkawuran da ta ɗauka tun bayan fara aiki.
A cewarsa, cikin shekara guda gwamnatin ƙaramar hukumar ta raba Naira miliyan 130 ga masu sana’o’i, ‘yan kasuwa da masu ƙananan harkokin kasuwanci, tare da gudanar da shirye-shiryen tallafa wa mabukata da kayan abinci.
Ya bayyana cewa an gudanar da matakai goma na shirin “Ounje Emi”, an kuma raba kayan abinci a lokutan Ramadan, Azumi da Eid-el-Kabir, baya ga tallafa wa zawarawa.
Shugaban ƙaramar hukumar ya kuma lissafa ayyukan ci gaba da suka haɗa da gyaran titin Jebba–Tapa–Oko Baba da magudanan ruwa, gyaran makarantar firamare ta U.N.A., gyaran magudanan ruwa a Freeman Road, gyaran makarantar Kadara Primary School, gyaran manyan bututun ruwa a Ebute Metta East da kuma girka fitilun hasken rana guda 410 a ƙarƙashin shirin Light Up Lagos Mainland.
Haka kuma ya ce an gyara sakatariyar ƙaramar hukumar, an sayo motocin aiki ga kansiloli, ma’aikata da ƙungiyoyin kasuwanni, tare da kula da hanyoyi da dama a faɗin ƙaramar hukumar.
Ɗaya daga cikin waɗanda suka ci gajiyar shirin, Abibat Bamgboye, ta yaba da wannan mataki, tana mai cewa irin wannan tallafi bai taɓa faruwa ba a tarihin ƙaramar hukumar, tare da fatan sauran ƙananan hukumomi za su kwaikwayi wannan tsari domin ƙarin jama’a su amfana.





