Anyi wa Zenith Bank Kutse an Kwashi Bayanan Kwastomomin Bankin
Daga Wakiliya
An shiga fargaba a ɓangaren harkokin banki a Najeriya bayan Zenith Bank ta tabbatar da cewa wasu masu kutse ta yanar gizo (hackers) sun samu damar shiga wasu daga cikin bayanan kwastomominta ba tare da izini ba.
A cikin wata sanarwa da bankin ya fitar ga kwastomominsa ranar Talata, ya ce an fara gudanar da bincike kan lamarin domin gano yadda aka samu kutse da kuma tantance irin bayanan da abin ya shafa.
Zenith Bank ta bayyana cewa bayanan da aka samu damar shiga sun haɗa da wasu adireshoshin imel (email) da kuma lambobin waya na wasu kwastomomi. Sai dai bankin ya ce har yanzu binciken yana gudana.
Bankin ya ƙara da cewa lamarin na daga cikin wani hari ta yanar gizo na duniya da ya shafi kamfanoni da cibiyoyi da dama a ƙasashe daban-daban.
Tun da farko, wasu kwastomomin Zenith Bank sun bayyana damuwa kan zargin samun shiga bayanansu ba tare da izininsu ba, lamarin da ya jawo bankin fitar da sanarwar.
A watan Maris na wannan shekarar, an kuma samu rahoton cewa masu kutse sun shiga bayanan wasu kwastomomin Remita, Sterling Bank, Providus Bank da wasu cibiyoyin kuɗi a Najeriya.
Bayan wannan lamarin, Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta yi alƙawarin gudanar da bincike kan matsalar satar bayanan. Sai dai zuwa yanzu ba a fitar da wani sabon bayani a hukumance kan sakamakon binciken ba.





