Daga Wakiliya
Lagos – Sarkin Shasha da ke ƙaramar hukumar Alimosho a Jihar Legas, Oba Nasiru Babatunde Ogunronbi, ya bukaci duk mazauna yankin ba tare da la’akari da ƙabila ko addini ba su mallaki tare da kiyaye Katin Zaɓe na Dindindin (PVC) domin su samu damar zaɓen shugabanni nagari a babban zaɓe mai zuwa.
Oba Ogunronbi ya yi wannan kira ne yayin da ya karɓi Sarkin Hausawan Shasha, Alhaji Ilyasu Isah Kira, da shugabannin al’ummar Hausawa daga ƙananan hukumomi shida na Alimosho a fadarsa.
Ya ce shiga cikin harkokin zaɓe hakki ne na kowane ɗan ƙasa, yana mai ƙara da cewa al’ummar Arewa mazauna Legas su mallaki katin zaɓensu tare da mara wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu baya domin sake zaɓensa a wa’adi na biyu. Haka kuma ya yi kira da a goyi bayan Dr. Kadiri Hamzat domin zama gwamnan Jihar Legas na gaba.
A nasa jawabin, Sarkin Hausawan Shasha, Alhaji Ilyasu Isah Kira, ya tabbatar da cewa al’ummar Hausawa za su ci gaba da wayar da kan jama’a kan rajistar masu zaɓe, rigakafin yara, tsaro da kuma zaman lafiya.
Shi ma Babban Sakataren Shugabannin Al’ummar Arewa na Alimosho, Ibrahim Abubakar Jagaba, ya ce Sarakunan Hausawa a ƙananan hukumomi shida za su ci gaba da wayar da kan jama’a kan muhimmancin mallakar katin zaɓe, shiga cikin zaɓe, da haɗin gwiwa da hukumomi domin tabbatar da zaman lafiya, tsaro da ci gaban al’umma.





