Daga Wakiliya
Wasu mazauna jihar Kano sun ce sun samu matsalolin idanu bayan amfani da wani maganin ido da aka raba musu kyauta mai suna “Miracle Eye: God is the Cure.”
Mutanen da suka yi magana da majiyar Wakiliya sun ce masu raba maganin sun yi ikirarin cewa yana magance cututtukan ido da kuma wasu matsalolin jiki.
A cewarsu, kafin a diga musu maganin a ido, ana ba su wani ruwa su sha, sannan a zuba musu wani a kunne tare da girgiza musu kai.
Ɗaya daga cikin waɗanda abin ya shafa ya ce washegari bayan amfani da maganin, idonsa ya yi ja, ya kumbura, yana fitar da dattin ido tare da ciwo mai tsanani, yayin da ganinsa ya fara dusashewa.
“Na yi zaton zan samu waraka, amma sai matsalata ta ƙaru. Ganina ya koma kamar an rufe shi da wani farin abu,” in ji shi.
Rahoton ya ce ana amfani da rabon maganin kyauta ne domin jawo hankalin mutane su sayi cikakken kwalin maganin ido kan naira 3,000, da kuma wani man shafawa da ake ikirarin yana magance cututtuka daban-daban kan naira 9,000.
Wata mata mai shekaru da ta yi amfani da maganin ta ce ta farka da kumburi da matsanancin ciwon ido bayan kwana biyu da fara amfani da shi.
Lokacin da wakiliyar Iconic Times, ta kai ziyara wurin da ake gudanar da rabon maganin, ta tarar masu gudanar da shirin sun bar wurin. Wani jami’in tsaro ya ce sun tashi sun koma wani wuri da basu bayyana ba.





