Muhsin Ibrahim ya ce, a matsayinsa na tsohon sanata kuma dattijo, ya kamata Shehu Sani ya rika yin taka-tsantsan da irin abubuwan da yake wallafawa saboda mutane da dama, musamman matasa, na kallonsa a matsayin abin koyi.
Hukumar Binciken Kasa ta Najeriya (NGSA) ta ce na'urorinta sun gano girgizar da misalin ƙarfe 11:23 na safe a cibiyar sa ido da take da ita a Utako, Abuja.
Idan na zama Gwamna zan aiwatar da tsarin ilimi irin na ƙasar Switzerland - Pantami; ya ce matashin da ya yi digiri na iya samun sama da Naira miliyan 200 a shekara ta hanyar ƙwarewa a AI da Cybersecurity
Odumeje ya kuma zargi gwamnoni da sanatoci da kare kalaman Shugaba Tinubu cewa, "Tun kafin a haife ni akwai yunwa a Najeriya," yana mai cewa a zaɓen 2027 ne za a tantance
Tinubu ya ce tun bayan hawansa mulki ya ba hukumomin yaƙi da cin hanci da rashawa da sauran hukumomin tsaro 'yancin gudanar da ayyukansu ba tare da tsoma bakin gwamnati ba.
Ya ce idan aka zaɓe shi, gwamnatinsa za ta fi mayar da hankali kan bunƙasa ilimi, samar da ayyukan yi da koyar da matasa sana’o’in zamani, maimakon dogaro da rabon kuɗi.