Ko ɗana ne ku ka kama, kada ku tausaya masa” – Gwamna Bala ya umarci jami’an tsaro su murƙushe masu haƙar ma’adinai a Bauchi ba bisa ƙa’ida ba

Daga Wakiliya

Gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed, ya umarci jami’an tsaro su tsaurara mataki kan masu haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba a faɗin jihar, yana mai cewa kada a nuna wa kowa wata alfarma idan aka same shi da hannu.

Yayin da yake karɓar bakuncin sabon Babban Kwamandan Runduna ta 3 ta Sojojin Najeriya kuma Kwamandan Operation Enduring Peace, Manjo Janar Maxwell Dangana, a Fadar Gwamnatin Bauchi ranar Laraba, gwamnan ya ce haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba na daga cikin manyan abubuwan da ke haddasa matsalar tsaro a jihar.

Bala Mohammed ya buƙaci jami’an tsaro su ƙara ƙaimi wajen tattara bayanan sirri da kuma kamo duk masu hannu a wannan aiki ba tare da la’akari da matsayinsu ba.

“Ina so ku ƙara ƙaimi wajen tattara bayanan sirri. Kada ku tausaya wa kowa. Ko da ɗana ne yake da hannu a haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba, ku ɗauki mataki a kansa,” in ji gwamnan.

Ya kuma yi zargin cewa wasu masu faɗa a ji da masu ruwa da tsaki na cin moriyar haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba saboda ribar da ake samu daga harkar, lamarin da ya ce na ci gaba da kawo cikas ga ƙoƙarin tabbatar da zaman lafiya a wasu sassan jihar.

Gwamnan ya tabbatar da cewa gwamnatin jihar za ta ci gaba da tallafa wa hukumomin tsaro, yana mai bayyana cewa za a yi amfani da wani ɓangare na kuɗin tallafin tsaro na naira biliyan uku da Gwamnatin Tarayya ta bai wa jihohi wajen sayen motocin aiki domin ƙarfafa ayyukan tsaro.

Da yake mayar da martani, Gwamna Bala Mohammed ya ce an riga an bayar da kwangilar gina hanyar zuwa garin Mansur, yana mai bayyana fatan cewa aikin zai sauƙaƙa zirga-zirga tare da inganta ayyukan tsaro.

Haka kuma ya buƙaci Rundunar Sojin Najeriya ta kafa ƙarin sansanonin soja a wasu muhimman yankuna da suka haɗa da Azare da Tafawa Balewa domin ƙarfafa tsaro da inganta saurin mayar da martani ga barazanar tsaro.

DA DUMI-DUMI

Ba zan sake komawa Najeriya ba ko za a ba ni kyautar sama da ƙasa’ -inji ‘Yar Najeriyar da ta rasa ‘ya’yanta biyu sakamakon...

Ta ce ba talauci ko neman kuɗi ne ya sa ta bar Najeriya ba, sai dai abubuwan baƙin ciki da ta fuskanta bayan mutuwar 'ya'yanta biyu cikin ɗan gajeren lokaci.

EFCC ta rufe asusun gwamnatin Osun kwanaki 10 kafin zaɓen gwamna

Matakin ya zo ne sa'o'i kaɗan bayan Gwamnan Jihar Osun, Ademola Adeleke, ya zargi EFCC da shirin daskarar da asusun gwamnatin jihar da kuma na wasu manyan jami'an gwamnati gabanin zaɓen gwamnan jihar da za a gudanar ranar 15 ga Agusta

Gwamnatin Nigeria ta ƙaddamar da dandalin rajistar haihuwa da mutuwa ta yanar gizo

Gwamnatin ta ce samun ingantacciyar shaidar zama ɗan ƙasa na taimakawa wajen samun damar kiwon lafiya, ilimi, fasfo, ayyukan kuɗi da sauran shirye-shiryen gwamnati.

Sarkin Yarabawa a Legas ya gana da Hausawan Arewa mazauna Legas, ya bukace su su mallaki PVC domin mara wa Tinubu baya a 2027

Oba Ogunronbi ya yi wannan kira ne yayin da ya karɓi Sarkin Hausawan Shasha, Alhaji Ilyasu Isah Kira, da shugabannin al'ummar Hausawa daga ƙananan hukumomi shida na Alimosho a fadarsa.

Fiye da Mutum 1,000 Sun Amfana da Tallafin miliyan ɗai-dai da Kayan Sana’o’i a Lagos

Tallafin ya haɗa da kuɗi, injinan ɗinki, firiza, injinan niƙa, injinan yin abin sha, murhun gas, tare da kayan abinci kamar shinkafa, doya, ƙwai da taliyar noodles.

Kanun Labarai

Tinubu ya amince da ƙarin albashi ga jami’an sojin Najeriya, wasu kashi 30, wasu 50 wasu 80

Tinubu ya kuma buƙaci jami'an sojin su ɗauki wannan ƙarin albashi a matsayin wata alama ta godiyar gwamnati bisa hidimar da suke yi wa ƙasa, yana mai bayyana fatan cewa tare za su yi nasara a kan masu neman tayar da zaune tsaye a Najeriya.

Zaɓen 2027: “A Ganinmu Tinubu Ya Gaza” — Ƙungiyar Igbo Ta Yi Watsi Da Ikirarin Uzodimma Da Umahi Na Goyon Bayan Tinubu a Kudu...

Ƙungiyar ta kuma buƙaci jami'an gwamnati daga Kudu maso Gabas su mayar da hankali kan ayyukan da kundin tsarin mulki ya ɗora musu da kuma magance matsalolin tattalin arzikin al'umma, maimakon yin magana a madadin dukkan 'yan Igbo kan batutuwan siyasa.

Zaɓen 2027 ya riga ya ƙare – Uba Sani ya yi wa Tinubu alƙawarin kashi 95% na ƙuri’un Kaduna

A cewarsa, ya taɓa bayyana hakan watanni biyu da suka gabata kuma har yanzu babu wanda ya kawo hujjar da ta karyata ikirarinsa.
spot_img

Labarai masu alaka

Sauran bangarori

spot_imgspot_img