Gwamnatin Tarayya ta ƙaddamar da dandalin rajistar haihuwa da mutuwa ta yanar gizo
Daga Wakiliya
Gwamnatin Tarayya ta ƙaddamar da VitalReg, wani sabon dandali na yanar gizo da zai ba ‘yan Najeriya damar yin rajistar haihuwa da mutuwa cikin sauƙi ba tare da wahalar dogayen layuka ko takardu masu yawa ba.
Ta hannun Hukumar Kidaya ta Ƙasa (NPC), dandalin zai bai wa jama’a damar yin rajistar haihuwa da mutuwa, neman takardar shaidar haihuwa (Birth Attestation), gyara bayanai, tantance sahihancin takardun haihuwa da kuma samun wasu hidimomin rajistar jama’a ta yanar gizo.
Gwamnatin ta ce samun ingantacciyar shaidar zama ɗan ƙasa na taimakawa wajen samun damar kiwon lafiya, ilimi, fasfo, ayyukan kuɗi da sauran shirye-shiryen gwamnati.
Masu buƙatar amfani da sabis ɗin za su iya shiga dandalin ta selfservice.nationalpopulation.gov.ng, ko kuma su ziyarci cibiyoyin rajista na NPC da ke faɗin ƙasar domin samun taimako.




