EFCC ta rufe asusun gwamnatin Osun kwanaki 10 kafin zaɓen gwamna
Daga Wakiliya
Hukumar Yaƙi da Yi Wa Tattalin Arzikin Ƙasa Ta’annati (EFCC) ta sanya takunkumin “Post No Debit” a kan wani asusun Gwamnatin Jihar Osun da ke Bankin First Bank, lamarin da ke nufin ba za a iya cire kuɗi daga asusun ba.
Rahotanni sun ce ana amfani da asusun wajen biyan albashin ma’aikatan gwamnati.
Matakin ya zo ne sa’o’i kaɗan bayan Gwamnan Jihar Osun, Ademola Adeleke, ya zargi EFCC da shirin daskarar da asusun gwamnatin jihar da kuma na wasu manyan jami’an gwamnati gabanin zaɓen gwamnan jihar da za a gudanar ranar 15 ga Agusta.
A cikin wata sanarwa da Kwamishinan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai na jihar, Kolapo Alimi, ya fitar, gwamnatin jihar ta ce babu wata hujjar doka da ta ba EFCC ikon daskarar da asusun gwamnatin jihar, tana mai cewa matakin na iya kawo cikas ga ayyukan gwamnati.
Wata majiya da ke kusa da gwamnatin jihar, wadda ta nemi a sakaya sunanta, ta tabbatar wa jaridar Vanguard cewa an riga an daskarar da asusun.
Majiyar ta ce gwamna zai yi wa manema labarai bayani kan lamarin domin sanar da jama’a halin da ake ciki.
Har zuwa lokacin da aka wallafa wannan rahoto, EFCC ba ta fitar da wata sanarwa a hukumance ba kan lamarin, kuma ba a bayyana dalilin da ya sa aka sanya takunkumin kan asusun ba.





