Tinubu ya amince da ƙarin albashi ga jami’an sojin Najeriya, wasu kashi 30, wasu 50 wasu 80

Tinubu ya amince da ƙarin albashi ga jami’an sojin Najeriya

Daga Wakiliya

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya amince da ƙarin albashi ga jami’an rundunar sojin Najeriya da ya kai tsakanin kashi 30 zuwa 80 cikin ɗari, a wani mataki da gwamnatin tarayya ta ce na inganta jin daɗin dakarun ƙasar.

Sanarwar da Fadar Shugaban Ƙasa ta fitar ta ce kusan jami’ai da sojoji 250,000 ne za su amfana da sabon tsarin albashin, wanda zai fara aiki daga ranar 1 ga Satumban 2026.

A ƙarƙashin sabon tsarin, manyan jami’an da ke sama da muƙamin Kanal, ciki har da Birgediya Janar, Manjo Janar, Laftanar Janar da Janar, za su samu ƙarin albashi na kashi 30 cikin ɗari.

Jami’an da ke daga muƙamin Kanal zuwa Warrant Officer kuwa za su samu ƙarin albashi na kashi 50 cikin ɗari, yayin da sojoji daga muƙamin Private zuwa Staff Sergeant za su samu ƙarin albashi mafi yawa, wato kashi 80 cikin ɗari.

Fadar Shugaban Ƙasa ta ce sabon tsarin zai ƙara kuɗin albashin sojojin Najeriya na shekara daga naira biliyan 660 zuwa naira biliyan 924.

A cewar Shugaba Tinubu, gwamnatinsa na ci gaba da yaba wa jajircewa da sadaukarwar jami’an tsaro wajen yaƙi da ta’addanci, garkuwa da mutane da kuma ‘yan bindiga a sassa daban-daban na ƙasar.

Ya ce dole ne gwamnati ta tallafa wa waɗanda ke sadaukar da rayuwarsu domin kare lafiya da dukiyoyin ‘yan Najeriya, yana mai jaddada cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da ba rundunar soji kayan aiki na zamani da kuma inganta walwalarsu.

Shugaban ya kuma bayyana cewa babu wata ƙasa da za ta iya samun ci gaba ba tare da ingantaccen tsaro ba, yana mai cewa gwamnati za ta ci gaba da amfani da dukkanin ƙarfin rundunonin tsaro domin murƙushe barazanar tsaro da kare rayuka da dukiyoyin al’umma.

Tinubu ya kuma buƙaci jami’an sojin su ɗauki wannan ƙarin albashi a matsayin wata alama ta godiyar gwamnati bisa hidimar da suke yi wa ƙasa, yana mai bayyana fatan cewa tare za su yi nasara a kan masu neman tayar da zaune tsaye a Najeriya.

DA DUMI-DUMI

Zaɓen 2027: “A Ganinmu Tinubu Ya Gaza” — Ƙungiyar Igbo Ta Yi Watsi Da Ikirarin Uzodimma Da Umahi Na Goyon Bayan Tinubu a Kudu...

Ƙungiyar ta kuma buƙaci jami'an gwamnati daga Kudu maso Gabas su mayar da hankali kan ayyukan da kundin tsarin mulki ya ɗora musu da kuma magance matsalolin tattalin arzikin al'umma, maimakon yin magana a madadin dukkan 'yan Igbo kan batutuwan siyasa.

Zaɓen 2027 ya riga ya ƙare – Uba Sani ya yi wa Tinubu alƙawarin kashi 95% na ƙuri’un Kaduna

A cewarsa, ya taɓa bayyana hakan watanni biyu da suka gabata kuma har yanzu babu wanda ya kawo hujjar da ta karyata ikirarinsa.

Sojin Ruwa da Kwastam Sun Kama Buhunan Shinkafa 518 da Ake Zargin An Shigo da Su Ba Bisa Ka’ida Ba

Rundunar Sojin Ruwan ta tabbatar da cewa za ta ci gaba da hada kai da sauran hukumomin tsaro wajen yaki da fasa-kauri da sauran ayyukan haramtattu a yankunan ruwan kasar.

Zaɓen 2027: Sarakuna a Kwara Sun Bayyana Goyon Bayansu Ga APC, Za Su Taya Jam’iyyar Yaƙin Neman Zaɓe

Shi ma Olofa na Offa, Oba Mufutau Gbadamosi Esuwye, ya bayyana kwarin gwiwarsa cewa 'yan takarar APC a jihar Kwara za su samu nasara a zaɓen 2027.

Ku Rika Zuwa Filin Jirgin Sama Aƙalla Sa’o’i Uku Kafin Tashin Jirginku – NCAA Ta Gargadi Matafiya

Ya kuma buƙaci fasinjoji da su yi amfani da tsarin rajista ta intanet (online check-in) idan hakan ya yiwu, tare da zaɓen kujerarsu tun kafin isa filin jirgin.

Kanun Labarai

2027: Matasan APC na Arewa Sun Yi Barazanar Janye Goyon Baya Ga Tinubu, Saboda Zargi Ana Nuna Musu Wariya

A cewar ƙungiyar, ta umarci shugabannin ƙungiyoyin goyon bayan APC 1,378 da ke jihohin Arewa 19 da Babban Birnin Tarayya Abuja su fara tattaunawa kan yiwuwar janye goyon baya ga takarar Tinubu ta wa'adi na biyu idan ba a saurari korafinsu ba.

UAE Za Ta Zuba Jarin Dala Biliyan $71 a Afirka, Domin Zurfafa Haɗin Gwiwa da Nahiyar

Ya jaddada cewa UAE za ta ci gaba da aiki tare da gwamnatocin Afirka da kamfanoni masu zaman kansu wajen aiwatar da ayyukan da za su haɓaka ci gaba mai ɗorewa da samar da damarmakin tattalin arziƙi ga nahiyar.

Matsalar Rashin Amincewa Da Ke Hana Kasuwancin Intanet Bunƙasa a Najeriya Musamman Arewa

A yau, aika kuɗi ta banki ko manhajojin kuɗi ya zama abu mai sauƙi a Najeriya. Amma sauƙin tura kuɗi ba yana nufin an magance matsalar kasuwanci ba.
spot_img

Labarai masu alaka

Sauran bangarori

spot_imgspot_img