Daga Wakiliya
Wata ‘yar Najeriya da ke zaune a Birtaniya ta ce ba za ta koma Najeriya ba ko da za a ba ta fam miliyan 15 (£15m), tana mai cewa rasa ‘ya’yanta biyu sakamakon abin da ta zargi sakacin likitoci ne ya sa ta ɗauki wannan matsaya.
Matar ta bayyana hakan ne a wata hira da aka yi da ita a kan titi, wadda wani mai wallafa bidiyo a shafukan sada zumunta ya yi, kuma bidiyon ya bazu sosai a intanet.
Ta ce ba talauci ko neman kuɗi ne ya sa ta bar Najeriya ba, sai dai abubuwan baƙin ciki da ta fuskanta bayan mutuwar ‘ya’yanta biyu cikin ɗan gajeren lokaci.
A cewarta, mutuwar yaran ta faru ne sakamakon abin da ta kira sakacin likitoci, lamarin da ya jefa iyalinta cikin babban baƙin ciki kuma har yanzu bai gushe daga zuciyarta ba.
Matar ta ce wannan abu ya sa ta rasa amincewa da tsarin kiwon lafiyar Najeriya, tana mai cewa babu adadin kuɗin da zai sa ta sake komawa ta zauna a ƙasar.
Kalaman nata sun haifar da muhawara a shafukan sada zumunta, inda wasu suka nuna alhini da juyayi kan abin da ya faru da ita, yayin da wasu kuma suka ce lamarin ya sake jawo hankali kan ƙalubalen da ake fuskanta a fannin kiwon lafiya da kuma buƙatar ƙara ɗaukar matakan tabbatar da ingancin aikin likitoci a Najeriya.
Wakiliya ba ta samu wata hujja mai zaman kanta da ke tabbatar da zargin sakacin likitocin da matar ta yi ba.





