Abunda muka sani game da rade-radin Auren Ronaldo da Georgina a wannan makon

DA DUMI-DUMI

Ana rade-radin Cristiano Ronaldo da Georgina Rodríguez za su yi aure a ƙarshen mako, amma har yanzu ba su tabbatar ba

An dade ana ta rade-radin cewa fitaccen ɗan wasan ƙwallon ƙafa Cristiano Ronaldo da abokiyar zamansa Georgina Rodríguez za su yi aure, bayan kusan shekara 10 suna tare.

Rahotanni daga kafafen yaɗa labarai na Portugal sun ce ana sa ran za a gudanar da bikin a ranar Asabar, 8 ga watan Agusta, a garin Funchal da ke tsibirin Madeira, inda Ronaldo ya fito.

Sai dai har yanzu Ronaldo ko Georgina ba su fitar da wata sanarwa da ke tabbatar da cewa za a yi auren.

Me ya sa aka zaɓi Madeira?

Madeira na da muhimmanci ga Ronaldo domin a can aka haife shi kuma ya taso kafin ya fara shahara a wasan ƙwallon ƙafa.

A tsibirin ne kuma ake da gidan tarihin Cristiano Ronaldo da kuma filin jirgin saman da aka sanya wa sunansa.

Su wa ake sa ran za su halarta?

Har yanzu babu jerin sunayen baƙi da aka tabbatar a hukumance.

Sai dai wasu rahotanni da suka bazu a shafukan sada zumunta sun yi ikirarin cewa fitattun mutane da dama za su halarta, ciki har da Rio Ferdinand, Erling Haaland, Lamine Yamal, Vin Diesel, Piers Morgan, Vinícius Júnior, Kylian Mbappé, Jennifer Lopez, Khabib Nurmagomedov, IShowSpeed, Drake da Travis Scott.

Sai dai babu wata hujja da ta tabbatar da wannan jerin sunaye.

Wasu masu amfani da shafukan sada zumunta sun kuma lura cewa ba a ambaci Lionel Messi ba, lamarin da ya janyo ce-ce-ku-ce. Amma babu wata alama da ke nuna cewa an gayyace shi ko kuma zai halarci bikin.

Rahotanni sun ce ana sa ran bikin zai kasance na sirri, tare da ‘ya’yansu biyar, iyalai da kuma abokai na kusa.

 

Me za a ci a bikin?

Wasu kafafen yaɗa labarai na Portugal sun ce ana iya gabatar da abincin gargajiyar Madeira tare da wasu nau’ikan abinci na zamani da ƙwararrun masu girki za su tanada.

Sai dai har yanzu babu wani bayani da aka tabbatar a hukumance kan abin da za a gabatar a bikin.

- Advertisement -spot_img

Leave a Reply

- Advertisement -spot_img
Za ku so wadannan

BRAZIL: Mutumin da matarsa ta yanke wa azzakari zai sake aurenta

Yanzu haka, Gilberto na shirin sake aurenta, inda zai yi amfani da kuɗin diyya da ya samu bayan an yaɗa hotunan raunukan da ya samu a intanet ba tare da izininsa na yaɗawa ba.
- Advertisement -spot_img

Labarai masu alaka

- Advertisement -spot_img