Kabilar Bodi na Ethiopia na shirya gasar wanda ya fi ƙiba a duk shekara, mata kuma na zuwa domin zaɓen miji
Daga Wakiliya
Ko kun san a cikin Garin kwarin Omo da ke ƙasar Ethiopia, kabilar Bodi na gudanar da wata al'ada ta musamman duk shekara mai suna Ka'el, wadda ake yi domin murnar sabuwar shekara.
A wannan biki, ana shirya gasa tsakanin maza domin a ga wanda ya fi kowa ƙiba.
Watanni shida kafin bikin, kowace daga cikin ƙabilun Bodi 14 tana zaɓar saurayi guda ɗaya da zai shiga gasar. Daga wannan lokaci, aikin mutumin shi ne cin abinci da hutawa kawai. Ba ya yin wani aiki ko motsa jiki, yayin da matan ƙabilar ke kawo masa abinci.
Abincin da masu gasar ke ci ya ƙunshi madara da jinin shanu. Kabilar Bodi ba sa yanka shanunsu saboda suna ɗaukarsu masu tsarki. Maimakon haka, suna fitar da ɗan jini daga jikin saniya ba tare da kashe ta ba, sannan su haɗa shi da madara domin sha.
Bayan watanni shida, masu gasar kan yi ƙiba sosai. A ranar bikin, sukan shafa toka da laka a jikinsu tare da sanya kayan gargajiya, sannan su riƙa zagaya wani itace mai tsarki yayin da dattawa da sauran jama'a ke kallonsu.
Matan ƙabilar ma kan halarci bikin domin kallon masu gasar da kuma zaɓen waɗanda za su aura. A al'adar Bodi, ana ɗaukar namiji mai ƙiba a matsayin mafi kyau da kyan hali.
Wanda ya lashe gasar ba ya samun kuɗi ko wata kyauta. Sai dai yana samun babban abin da kabilar Bodi ke darajtawa fiye da komai – girmamawa da martaba daga al'ummarsa har ƙarshen rayuwarsa.





