Idan na zama Gwamna zan aiwatar da tsarin ilimi irin na ƙasar Switzerland – mai digiri na iya samun sama da miliyan 200 -Pantami

Idan na zama Gwamna zan aiwatar da tsarin ilimi irin na ƙasar Switzerland – matashin da ya yi digiri na iya samun sama da Naira miliyan 200 a shekara ta hanyar ƙwarewa a AI da Cybersecurity -Pantami

Daga Wakiliya

Tsohon Ministan Sadarwa da Tattalin Arzikin Zamani, Farfesa Isa Ali Pantami, ya ce ci gaban ɗan Adam ya kamata ya zama babban abin da gwamnati za ta fi mayar da hankali a kai fiye da gina manyan gine-gine.

Pantami ya bayyana hakan ne yayin wata hira, inda ya ce duk da cewa gwamnatocin baya sun yi ƙoƙari wajen gina jami'o'i, filayen jiragen sama da sauran manyan ayyuka, mataki na gaba shi ne bunƙasa rayuwar al'umma, domin a cewarsa ɗan Adam shi ne mafi daraja cikin halittu.

Ya ce Arewacin Najeriya ya fi mayar da hankali wajen gina birane maimakon gina mutane, yana mai jaddada cewa ci gaba mai ɗorewa ba zai samu ba sai an saka hannun jari a ilimi da ƙwarewar matasa.

Pantami ya bayyana cewa yana goyon bayan tsarin ilimi irin na ƙasar Switzerland, wanda ke haɗa karatun digiri da koyon ƙwarewar zamani. A cewarsa, wanda ya kammala karatun Sociology amma bai samu aiki ba, idan ya yi horo na shekara ɗaya ko biyu a fannoni kamar Cybersecurity, Artificial Intelligence (AI), Microsoft, Blockchain ko Internet of Things (IoT), zai iya samun aikin yi daga ko'ina cikin duniya.

Ya ƙara da cewa irin waɗannan ƙwarewa na iya bai wa mutum damar samun kusan dala 150,000 a shekara, wanda ya ce ya haura Naira miliyan 200 idan aka mayar da kuɗin zuwa na Najeriya.

Pantami ya kuma bayyana cewa inganta ilimi, sake horas da malamai tare da kyautata albashinsu, ƙarfafa neman halal da samar wa matasa yanayin da zai ba su damar bunƙasa su ne ginshiƙan ci gaban al'umma.

Har ila yau, ya ce watsi da mata na daga cikin manyan matsalolin da ke hana al'umma ci gaba. Ya yi nuni da cewa muhimmancin mace ya fi na jami'a, yana mai kawo misalin marigayi Sardaunan Sakkwato, Sir Ahmadu Bello, wanda ya kafa Jami'ar Ahmadu Bello da ke Zariya, yana cewa shi ma mace ce ta raina shi kafin ya zama jagora.

DA DUMI-DUMI

Abunda muka sani game da rade-radin Auren Ronaldo da Georgina a wannan makon

Wasu masu amfani da shafukan sada zumunta sun kuma lura cewa ba a ambaci Lionel Messi ba, lamarin da ya janyo ce-ce-ku-ce.

Duk mai goyon bayan gwamnatin Tinubu an ba shi cin hanci — Fasto Odumeje

Odumeje ya kuma zargi gwamnoni da sanatoci da kare kalaman Shugaba Tinubu cewa, "Tun kafin a haife ni akwai yunwa a Najeriya," yana mai cewa a zaɓen 2027 ne za a tantance

Har Naji kunya  – Tinubu ya umarci EFCC ta janye umarnin kotu na rufe asusun Gwamnatin Osun

Tinubu ya ce tun bayan hawansa mulki ya ba hukumomin yaƙi da cin hanci da rashawa da sauran hukumomin tsaro 'yancin gudanar da ayyukansu ba tare da tsoma bakin gwamnati ba.

Jami’in FRSC ya karɓi N30,000 daga hannuna, sai kuma ya manta wayarsa a cikin motata

Jami'in FRSC ya karɓi N30,000 daga hannuna, sai kuma ya manta wayarsa a cikin motata"

Allah da ya ɗauki ran Abacha kafin zaɓe yana kallon ka – Dino Melaye ya gargadi Tinubu kan zaɓen 2027

A cewarsa, akwai abin da ya kira "ikon Allah a cikin al'amuran ɗan Adam", yana mai cewa babu wani shiri na siyasa da zai iya rinjayar nufin Allah.

Kanun Labarai

Anyi wa Zenith Bank Kutse an Kwashi Bayanan Kwastomomin Bankin

Zenith Bank ta bayyana cewa bayanan da aka samu damar shiga sun haɗa da wasu adireshoshin imel (email) da kuma lambobin waya na wasu kwastomomi. Sai dai bankin ya ce har yanzu binciken yana gudana.

Abubuwa 6 da za ku iya sha kafin barci domin taimakawa wajen daidaita sikarin jini da rage haɗarin kamuwa da ciwon suga

• Ka riƙa shan isasshen ruwa. • Ka yi barci na awa 7 zuwa 9 a kullum. • Ka gama cin abinci awa 2 zuwa 3 kafin kwanciya idan zai yiwu. • Idan yunwa ta taso da dare, ka zaɓi ɗan abin ci mai gina jiki maimakon kayan zaki ko abubuwan sha masu sukari.

Mutane da dama sun samu matsalolin idanu bayan amfani da maganin ido da aka raba kyauta a Kano

Na yi zaton zan samu waraka, amma sai matsalata ta ƙaru. Ganina ya koma kamar an rufe shi da wani farin abu," in ji shi.
spot_img

Labarai masu alaka

Sauran bangarori

spot_imgspot_img