Daga Wakiliya
An sake jin wata ƙaramar girgizar ƙasa a wasu sassan Babban Birnin Tarayya, Abuja, a ranar Talata, lamarin da ya sa gine-gine suka ɗan girgiza tare da jefa wasu mazauna cikin fargaba.
Hukumar Binciken Kasa ta Najeriya (NGSA) ta ce na'urorinta sun gano girgizar da misalin ƙarfe 11:23 na safe a cibiyar sa ido da take da ita a Utako, Abuja.
A cewar hukumar, girgizar ta samo asali ne daga zurfin kusan kilomita ɗaya ƙarƙashin ƙasa, inda ta bazu zuwa kusan kilomita huɗu cikin daƙiƙa biyar.
Hukumar ta bayyana cewa ƙarfin girgizar ya kai mataki na ɗaya zuwa na biyu (I–II) a ma'aunin Mercalli, wanda ke nuna cewa girgizar ba ta da ƙarfi sosai kuma ba ta zama barazana ga rayuka ko dukiyoyi, sai dai tana iya jawo tsoro ko rashin jin daɗi ga jama'a.
A wata sanarwa da mai taimaka wa Ministan Ma'adanai na Tarayya kan harkokin yaɗa labarai, Lara Owoeye-Wise, ta fitar, Ministan Ma'adanai, Dele Alake, ya buƙaci Hukumar NGSA ta ci gaba da sa ido kan duk wani sauyi da ya shafi girgizar ƙasa a Abuja tare da riƙa ba da rahoto a kai a kai.
Ministan ya kuma shawarci mazauna Abuja da su ci gaba da gudanar da harkokinsu na yau da kullum ba tare da fargaba ba, yana mai tabbatar da cewa gwamnati na ci gaba da sanya ido kan lamarin domin kare rayuka da dukiyoyi.





