Daga Wakiliya
Dan Majalisar Wakilan Amurka daga jam'iyyar Republican, Andy Ogles, ya sha kaye a zaɓen fidda gwani da aka gudanar a jihar Tennessee, duk da samun cikakken goyon bayan Shugaba Donald Trump.
Abokin hamayyarsa, Charlie Hatcher, tsohon Kwamishinan Aikin Gona na jihar, ya yi nasara da tazarar ƙuri'u bayan kidayar kusan kashi 90 cikin 100 na sakamakon zaɓen.
Kafin zaɓen, Trump ya bayyana cikakken goyon bayansa ga Ogles, amma hakan bai hana shi faduwa ba. Wannan ya sa Ogles ya zama ɗaya daga cikin ‘yan takarar da Trump ya mara wa baya amma suka gaza cin zaɓen fidda gwani a wannan makon.
Andy Ogles ya sha suka a baya saboda kalaman da ya yi kan Musulmi. A watan Maris ya rubuta a shafinsa na X cewa, “Musulmi ba su da gurbi a cikin al'ummar Amurka. Ra'ayin zaman tare tsakanin addinai ƙarya ne.”
A shekarar 2024 kuma, lokacin da wani mai fafutuka ya tambaye shi ko ya ga hotunan yara Falasɗinawa da aka kashe a hare-haren bama-bamai da Amurka ke tallafawa, Ogles ya amsa da cewa: “Ina ganin ya kamata a kashe su duka.” Kalaman sun jawo masa suka daga bangarori daban-daban.
Charlie Hatcher kuwa ya yi watsi da irin waɗannan kalamai, yana mai cewa akwai Musulman Amurka masu bin doka kuma har da sojojin Musulmi da ke yi wa ƙasar hidima cikin ƙwarewa.
A babban zaɓen watan Nuwamba, Hatcher zai fafata da ɗan takarar jam'iyyar Democrat, Chaz Molder, magajin garin Columbia a jihar Tennessee. Duk da cewa mazabar na karkata ga Republican, jam'iyyar Democrat na fatan amfani da rashin gamsuwar wasu masu zaɓe kan tattalin arziki da yaƙin Iran domin samun nasara.





