Daga Wakiliya
Malamin jami'a da ke Jamus ya soki Shehu Sani kan sakon da ya yi game da mata marasa aure masu shekara 28
Muhsin Ibrahim, marubuci kuma malami a Jami'ar Cologne da ke Jamus, ya soki tsohon Sanatan Kaduna ta Tsakiya, Shehu Sani, kan wasu sakonnin da ya wallafa a kafafen sada zumunta, yana mai cewa sun kunshi raina mata kuma ba su dace da matsayinsa ba.
A cikin wani dogon sako da ya wallafa, Ibrahim ya ce ya dade yana girmama Shehu Sani saboda gwagwarmayarsa da rubuce-rubucensa. Ya ce tun sama da shekara goma da suka wuce ya fara mu'amala da shi a shafin Twitter (X), har ma tsohon sanatan ya yi masa alkawarin ba shi kyautar wani littafinsa.
Sai dai ya ce a baya-bayan nan ya lura da cewa sakonnin Shehu Sani a kafafen sada zumunta sun fara zama abin takaici, inda yake yawan yin barkwanci kan batutuwa masu muhimmanci tare da wallafa abubuwan da ba su dace ba.
Muhsin Ibrahim ya ce, a matsayinsa na tsohon sanata kuma dattijo, ya kamata Shehu Sani ya rika yin taka-tsantsan da irin abubuwan da yake wallafawa saboda mutane da dama, musamman matasa, na kallonsa a matsayin abin koyi.
Ya kuma soki mutanen da suka nuna goyon baya ga wani sako da ya ce yana raina mata marasa aure masu shekara 28, yana mai cewa hakan rashin tausayi ne.
A cewarsa, ba duk mata ne rashin aure a wannan shekarun ya kasance zabinsu ba, yana mai tambayar ko mutane za su yi irin wannan dariya idan ‘yar uwarsu ko ‘yarsu ce ke cikin irin wannan hali.
Muhsin Ibrahim ya yi kira ga masu amfani da kafafen sada zumunta da su rika yin taka-tsantsan kan abubuwan da suke wallafawa da kuma irin sakonnin da suke goyon baya, yana cewa kalaman da ake yi a shafukan sada zumunta na da tasiri kuma suna bayyana irin halayen mutum.





