Allah da ya ɗauki ran Abacha kafin zaɓe yana kallon ka – Dino Melaye ya gargadi Tinubu kan zaɓen 2027

Daga Wakiliya

Tsohon Sanatan Kogi ta Yamma, Dino Melaye, ya gargadi Shugaba Bola Ahmed Tinubu da kada ya ɗauki zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2027 da wasa, yana mai cewa amincewar jam'iyyun siyasa kaɗai ba ta isa ta tabbatar da makomar kowane ɗan siyasa ba.

Melaye, wanda jigo ne a jam'iyyar ADC, ya bayyana hakan ne a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na 𝕏 a ranar Laraba.

Ya tuna da marigayi tsohon Shugaban Mulkin Soja, Janar Sani Abacha, yana cewa a lokacin rayuwarsa jiga-jigan jam'iyyun siyasa biyar da ke tashe a wancan lokaci sun amince da shi a matsayin ɗan takararsu na shugaban ƙasa.

Sai dai Melaye ya ce duk da hakan, Abacha ya rasu a shekarar 1998 kafin ya cika burinsa na komawa shugaban ƙasa ta hanyar zaɓe (farar hula).

A cewarsa, akwai abin da ya kira “ikon Allah a cikin al'amuran ɗan Adam”, yana mai cewa babu wani shiri na siyasa da zai iya rinjayar nufin Allah.

“Allah da ya kira (dauki ran) Abacha bai tafi omugwo ba. Tinubu ya kula,” in ji Melaye.

Kalmar “omugwo” kalma ce ta al'adar kabilar Igbo, wadda ke nufin lokacin da uwa ko suruka ke kula da mace bayan ta haihu.

Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, Shugaba Bola Tinubu ko Fadar Shugaban Ƙasa ba su fitar da wata sanarwa kan kalaman Dino Melaye ba.

DA DUMI-DUMI

Anyi wa Zenith Bank Kutse an Kwashi Bayanan Kwastomomin Bankin

Zenith Bank ta bayyana cewa bayanan da aka samu damar shiga sun haɗa da wasu adireshoshin imel (email) da kuma lambobin waya na wasu kwastomomi. Sai dai bankin ya ce har yanzu binciken yana gudana.

Abubuwa 6 da za ku iya sha kafin barci domin taimakawa wajen daidaita sikarin jini da rage haɗarin kamuwa da ciwon suga

• Ka riƙa shan isasshen ruwa. • Ka yi barci na awa 7 zuwa 9 a kullum. • Ka gama cin abinci awa 2 zuwa 3 kafin kwanciya idan zai yiwu. • Idan yunwa ta taso da dare, ka zaɓi ɗan abin ci mai gina jiki maimakon kayan zaki ko abubuwan sha masu sukari.

Mutane da dama sun samu matsalolin idanu bayan amfani da maganin ido da aka raba kyauta a Kano

Na yi zaton zan samu waraka, amma sai matsalata ta ƙaru. Ganina ya koma kamar an rufe shi da wani farin abu," in ji shi.

Ko ɗana ne ku ka kama, kada ku tausaya masa” – Gwamna Bala ya umarci jami’an tsaro su murƙushe masu haƙar ma’adinai a Bauchi...

"Ina so ku ƙara ƙaimi wajen tattara bayanan sirri. Kada ku tausaya wa kowa. Ko da ɗana ne yake da hannu a haƙar ma'adinai ba bisa ƙa'ida ba, ku ɗauki mataki a kansa," in ji gwamnan.

Ba zan sake komawa Najeriya ba ko za a ba ni kyautar sama da ƙasa’ -inji ‘Yar Najeriyar da ta rasa ‘ya’yanta biyu sakamakon...

Ta ce ba talauci ko neman kuɗi ne ya sa ta bar Najeriya ba, sai dai abubuwan baƙin ciki da ta fuskanta bayan mutuwar 'ya'yanta biyu cikin ɗan gajeren lokaci.

Kanun Labarai

EFCC ta rufe asusun gwamnatin Osun kwanaki 10 kafin zaɓen gwamna

Matakin ya zo ne sa'o'i kaɗan bayan Gwamnan Jihar Osun, Ademola Adeleke, ya zargi EFCC da shirin daskarar da asusun gwamnatin jihar da kuma na wasu manyan jami'an gwamnati gabanin zaɓen gwamnan jihar da za a gudanar ranar 15 ga Agusta

Gwamnatin Nigeria ta ƙaddamar da dandalin rajistar haihuwa da mutuwa ta yanar gizo

Gwamnatin ta ce samun ingantacciyar shaidar zama ɗan ƙasa na taimakawa wajen samun damar kiwon lafiya, ilimi, fasfo, ayyukan kuɗi da sauran shirye-shiryen gwamnati.

Sarkin Yarabawa a Legas ya gana da Hausawan Arewa mazauna Legas, ya bukace su su mallaki PVC domin mara wa Tinubu baya a 2027

Oba Ogunronbi ya yi wannan kira ne yayin da ya karɓi Sarkin Hausawan Shasha, Alhaji Ilyasu Isah Kira, da shugabannin al'ummar Hausawa daga ƙananan hukumomi shida na Alimosho a fadarsa.
spot_img

Labarai masu alaka

Sauran bangarori

spot_imgspot_img