Jami’in FRSC ya karɓi N30,000 daga hannuna, sai kuma ya manta wayarsa a cikin motata

Daga Wakiliya

Wani mutum Aliyu Nuhu ya ba da labarin abin da ya ce ya faru da shi yayin da yake tafiya daga Fatakwal zuwa Onitsha.

A cewarsa, da ya isa Owerri, wani jami'in Hukumar Kiyaye Haɗurra ta Kasa (FRSC) ya tsayar da shi, yana zarginsa da rashin sanya bel ɗin kujera (seatbelt).

Direban (Aliyu) ya ce ya roƙi jami'in da ya yi masa afuwa, yana mai alƙawarin cewa ba zai sake maimaita kuskuren ba, amma jami'in ya ƙi.

Ya ƙara da cewa jami'in ya yi barazanar ƙwace lasisin tuƙinsa tare da kai motarsa ofishin FRSC. Bayan doguwar roƙo, direban ya ce jami'in ya karɓi N30,000, wanda ya ce shi ne kaɗai kuɗin da ya rage masa domin sayen man fetur da sauran buƙatun tafiyarsa.

A cewarsa, bayan ya ci gaba da tafiya, yana dab da shiga Onitsha sai wayar da ke gefensa ta fara ƙara. Da ya duba, sai ya ga Samsung Galaxy S24, kuma bayan ya ɗaga kiran, ya gano cewa wayar ta jami'in FRSC ce da ya manta a cikin motarsa.

Yanzu, a cewar direban, jami'in yana ta roƙonsa da ya dawo masa da wayar.

Idan kai ne a irin wannan hali, me za ka yi?

DA DUMI-DUMI

Allah da ya ɗauki ran Abacha kafin zaɓe yana kallon ka – Dino Melaye ya gargadi Tinubu kan zaɓen 2027

A cewarsa, akwai abin da ya kira "ikon Allah a cikin al'amuran ɗan Adam", yana mai cewa babu wani shiri na siyasa da zai iya rinjayar nufin Allah.

Anyi wa Zenith Bank Kutse an Kwashi Bayanan Kwastomomin Bankin

Zenith Bank ta bayyana cewa bayanan da aka samu damar shiga sun haɗa da wasu adireshoshin imel (email) da kuma lambobin waya na wasu kwastomomi. Sai dai bankin ya ce har yanzu binciken yana gudana.

Abubuwa 6 da za ku iya sha kafin barci domin taimakawa wajen daidaita sikarin jini da rage haɗarin kamuwa da ciwon suga

• Ka riƙa shan isasshen ruwa. • Ka yi barci na awa 7 zuwa 9 a kullum. • Ka gama cin abinci awa 2 zuwa 3 kafin kwanciya idan zai yiwu. • Idan yunwa ta taso da dare, ka zaɓi ɗan abin ci mai gina jiki maimakon kayan zaki ko abubuwan sha masu sukari.

Mutane da dama sun samu matsalolin idanu bayan amfani da maganin ido da aka raba kyauta a Kano

Na yi zaton zan samu waraka, amma sai matsalata ta ƙaru. Ganina ya koma kamar an rufe shi da wani farin abu," in ji shi.

Ko ɗana ne ku ka kama, kada ku tausaya masa” – Gwamna Bala ya umarci jami’an tsaro su murƙushe masu haƙar ma’adinai a Bauchi...

"Ina so ku ƙara ƙaimi wajen tattara bayanan sirri. Kada ku tausaya wa kowa. Ko da ɗana ne yake da hannu a haƙar ma'adinai ba bisa ƙa'ida ba, ku ɗauki mataki a kansa," in ji gwamnan.

Kanun Labarai

Ba zan sake komawa Najeriya ba ko za a ba ni kyautar sama da ƙasa’ -inji ‘Yar Najeriyar da ta rasa ‘ya’yanta biyu sakamakon...

Ta ce ba talauci ko neman kuɗi ne ya sa ta bar Najeriya ba, sai dai abubuwan baƙin ciki da ta fuskanta bayan mutuwar 'ya'yanta biyu cikin ɗan gajeren lokaci.

EFCC ta rufe asusun gwamnatin Osun kwanaki 10 kafin zaɓen gwamna

Matakin ya zo ne sa'o'i kaɗan bayan Gwamnan Jihar Osun, Ademola Adeleke, ya zargi EFCC da shirin daskarar da asusun gwamnatin jihar da kuma na wasu manyan jami'an gwamnati gabanin zaɓen gwamnan jihar da za a gudanar ranar 15 ga Agusta

Gwamnatin Nigeria ta ƙaddamar da dandalin rajistar haihuwa da mutuwa ta yanar gizo

Gwamnatin ta ce samun ingantacciyar shaidar zama ɗan ƙasa na taimakawa wajen samun damar kiwon lafiya, ilimi, fasfo, ayyukan kuɗi da sauran shirye-shiryen gwamnati.
spot_img

Labarai masu alaka

Sauran bangarori

spot_imgspot_img